✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON2021: Senegal da Masar za su kara a wasan karshe

Kasashen biyu za su raba-raini a wasan karshe na gasar AFCON 2021.

Tawagar ’yan wasan kasar Senegal da kasar Masar za su fafata a wasan karshe na gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON2021), bayan samun nasara a kan Burkina Faso da mai masaukin baki Kamaru.

Senegal ta doke Burkina Faso da ci 3-1 a wasan kusa da na karshe, wanda hakan ya ba ta tikitin zuwa wasan karshe na gasar.

Masar kuwa ta yi waje-rod da Kamaru, wadda ita ce mai masaukin baki a bugun fenareti.

Wasan karshe na Gasar Kofin Nahiyar Afrika, zai dauki hankali matuka, ganin yadda fitattun ’yan wasa biyu, Sadio Mane daga Senegal da kuma Mohammed Salah daga Masar za su kara da juna.

’Yan wasan, wadanda dukkansu ’yan kungiyar Liverpool ne da ke Ingila, sun nuna bajinta da kwarewa wajen kai kasashensu wasan karshe na gasar.

Kasar Masar ta lashe kofin nahiyar Afrika har sau bakwai, wanda hakan ya sa wasu da dama ke ganin za ta iya sake lashewa a wannan karon.

Senegal kuwa ba ta taba lashe gasar ba, hasali ma a 2019 ta sha kashi a hannun Aljeriya a wasan karshe na gasar.

Sai dai a wannan karon ta kara zuwa wasan karshe na gasar, shin ko za ta iya kai bantenta?