✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Africa Magic zai yi fim a kan Aisha Buhari

Kamfanin, mallakin Multichoice, na shirin bullo da shirye-shirye domin Arewacin Najeriya.

Kamfanin shirye-shiyen talabijin na Afrika Magic na shirin yin fim din Aisha Buhari, a kan rayuwa da tarihin matar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Babban Jami’ar Kirkiro Shirye-shiyen Africa Magic, Busola Tejumola, ita ce ta sanar da batun fim din na Aisha Buhari a Kano, a gabanin taron baje kolin shirye-shirye na kwana biyu da kamfanin ya shirya.

“Yanzu lokaci ya yi da za a rika samun shirye-shirye masu matukar daukar hankali game da Arewacin Najeriya. Saboda haka yanzu ne lokacin da ya fi dacewa mu yi hadin gwiwa,” a cewar Busola.

Sanawar da kamfanin MultiChoice, mamallakan Africa Magic, ya fitar ta ce gudanar da taron baje kolin a daidai lokacin da ake taron shekara na Hukumar Yada Labarai ta Najeriya (BON), zai ba wa ainihin masu yin shirye-shirye damar ganawa da Africa Magic domin sayar da masa da hajojinsu.

Busola Tejumola, wacce ta sanar da shirin yin fim din Aisha Buhari, ta ce taron, wanda ya tattaro masa tsara shirye-shirye sama da 200 daga Arewacin Najeriya, zai samar da alfano ga kowane bangare.

“Taron baje kolin shirye-shirye na ‘Africa Magic Content Marketplace’ dandali ne da ke ba wa kowadanne irin masu samar da shirye-shirye damar ganawa da masu saye.

“Sannan dama ce a gare mu ta yi wa masu samar da shirye-shirye bayanai game da irin ingancin da muke bukata daga hajojin nasu.

“Taron zai zaga kowane yanki a fadin Najeriya, kuma yanzu lokaci ya yi da za a rika samun labarai masu matukar daukar hankali daga Arewacin Najeriya,” a cewarta.

Ko da yake ba ta yi bayani ko fin din na Aisha Buhari mai dogon zango ne ko gajeren zango ba.

Shirye-shiryen tashar Africa Magic dai galibi fina-finai ne da dangoginsu, da suka hada da masu gajeren da kuma masu dogon zango.

Kamfanin na gabatar da shirye-shirye a manyan harsunan Najeriya uku – Hausa, Igbo da Yarabanci – baya ga harshen turancin Ingilishi.