✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aguero zai yi watanni yana jinya — Barcelona

Babu shakka Aguero yana da muhimmiyar rawar da zai taka a kungiyar.

Matsaloli na ci gaba da yi wa kocin Barcelona Ronald Koeman kaka-gida kari a kan rasa fitaccen tauraron kungiyar, Lionel Messi wanda kungiyar ta kawo karshen zamansa na shekaru 21 tare da ita.

A halin yanzu dai Barcelona za ta tunkari kakar wasannin bana ta 2021/2022 ba tare da sabon dan wasan da kungiyar ta dauko daga Manchester City ba, Sergio Aguero.

Dan wasan na kasar Argentina ya ji rauni yayin motsa jiki a ranar Lahadi, inda ake tsammanin zai jinya ta watanni biyu zuwa uku.

A ranar Lahadin ce Barcelona ta sanar da cewa dan wasan wanda ya lashe gasar Copa America ta bana, ya samu rauni a kafarsa ta dama, inda bayan wasu gwaje-gwajen likitoci aka yi hasashen ba zai dawo fagen tamola ba har sai zuwa watan Nuwamba.

Dawowar Aguero fagen tamola wani lokaci nan kusa mai wuya, ganin yadda bai halarci taron gabatar da jawaban bankwana da Lionel Messi ya yi ba da kuma wasan da kungiyar ta samu nasara a Kofin Joan Gamper da ta kara da Juventus a daren Lahadi.

Da yake magana kan lamarin, Koeman ya bayyana takaicinsa kan raunin da Aguero ya samu wanda a cewarsa aikin al’ajibi ne kawai zai iya dawo da shi a nan kusa.

Koeman ya ce, “Babu yadda muka iya, dole mu jira har ya warke amma babu shakka wannan lamari koma baya ne a gare mu domin Aguero yana da muhimmiyar rawar da zai taka a kungiyar.”

Raunin Aguero dai shi ne na baya bayan nan a Barcelona, saboda akwai ’yan wasan kungiyar, Ansu Fati, da Ousman Dembele da ke jinya a halin yanzu bayan samun sauki da Philippe Coutinho ya yi.