✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ahmed Joda: Tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya ya rasu

Shugaban kwamitin mika mulki a 2015 ya rasu a asibiti yana da shekara 91.

Alhaji Ahmed Joda, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Shirye-Shiryen Mika Mulki ga Shugaba Muhammadu Buhari, ya rasu a ranar Juma’a.

Iyalansa sun tabbatar wa Aminiya cewa dattijon dan asalin Jihar Adamwa ya rasu ne a Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Yola, a Jihar ta Adamawa.

Alhaji Ahmed Joda wanda aka haifa a shekarar 1930 a Yola, Jihar Adamwa ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

Marigayin gogaggen ma’aikacin gwamnati ne, sannan kwararre a harkar gudanarwa kuma yana lambobin girmamawa na OFR da CON da kuma CFR.

Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da ya yi aiki a matsayin Babban Sakatare sun hada da Ma’aikatar Ilimi, Ma’aikatar Masana’antu da Ma’aikatar Sadarwa.

Sannan ya kasance Shugaban ko dan Kwamitin Daraktoci na hukumomi da kamfanonin gwamnati, ciki har da kamfanin mai na kasa (NNPC), hukumar samar da gas din girki (NLNG), Hukumar Sadarwa ta Tarayya (NCC), da sauransu.

Daga cikin kakannin Ahmed Joda, akwai Modibbo Raji, wanda sanannen malamin addinin Musulunci ne da ya yi zamani da Shehu Usmanu Danfodiyo.