✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ahmad Lawan ya kafa kwamitin yakin neman zaben Shugaban Kasa

Sanata Ahmed Lawan ya sake zage damtse kan neman takarar shugaban kasa.

Shugaban Majalisar Dattawa kuma daya daga cikin manema tikitin takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Sanata Ahmed Lawan, ya nada mambobin kwamitin yakin neman zabensa.

Wannan na zuwa ne bayan sanar da dan majalisa mai wakiltar shiyyar Abiya ta Arewa a Majalisar Dattawan, Sanata Orji Uzor Kalu, a matsayin jagoran kwamitin.

Tuni dai Sanata Orji Kalu ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC su tsayar da wanda zai yi wa APC takara daga yankin Arewa, idan har jam’iyyar na son yin nasara a zaben 2023.

Kalu ya ce matukar APC ta yi kuskuren tsayar da dan takara daga Kudu kamar ta yanki tikitin faduwa zaben ne.

Kazalika, tsohon Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Yariman Bakura, cikin wata tattaunawa da ya yi da Aminiya, ya ce yana san jam’iyyar tasu ta APC za ta tsaida dan takara daga arewa a zaben fid-da-gwanin da jam’iyyar za ta fara a ranar Litinin.

Sanata Lawan, wanda ya fara takarar kamar ba zai yi ba, yanzu ya kara kaimi tare da yin damara tamau kan ganin ya shiga Aso Rock a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya a 2023.

Daga cikin wadanda aka nada suna hada da Femi Fani Kayode, Uzor Kalu, Sanata Barau Jibrin da sauransu.

Tuni aka fara rade-radin cewar ‘yan siyasa da deliget daga yankin Kudu maso Gabas, Sanata Ahmed Lawan din za su zaba a matsayin wanda zai yi wa APC takara a babban zabe mai zuwa.