✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ahmed Musa ya rabu da kungiyar AlNassr FC ta Saudiyya

Ya taimaka wa kungiyar ta dauki kofin gasar kasar Saudiyya da kuma Super Cup.

Bayan kwashe shekaru biyu yana fafata wa a gasar kwallon kafa ta Kasar Saudiyya, shahararren dan wasan Najeriya Ahmed Musa, ya rabu da kungiyar AlNassr FC wadda ake yi wa lakabi da Najd Knight.

Kungiyar wadda ta lashe gasar kwarraru ta Saudiyya har sau takwas, da kanta ta bayyana hakan cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoban, inda ta yi wa dan wasa fatan alheri bayan sun raba gari cikin salama.

Cikin rahoton da kungiyar ta wallafa na bankwana, ta tattaro tarihi tun daga tarbar da aka yi masa a farkon zuwansa tare da kwallayen da ya jefa da kuma yadda ya ke motsa jiki.

A halin yanzu Ahmad Musa ba shi da wata kungiya da ya kulla yarjejeniya da ita, sai dai ana hasashen zai iya koma wa nahiyyar Turai domin ci gaba da taka leda kamar yadda yana nuna sha’awa.

Rahoton da BBC ta wallafa ya ce, Musa mai shekaru 28 ya buga wa kungiyar wasanni 58 inda ya samu nasarar jefa kwallo 11 da kuma bayar da taimako wajen kwallo 14 da aka ci.

Kazalika, ya kuma taimaka wa kungiyar ta dauki kofin gasar kasar Saudiyya da kuma Super Cup dinta.

Kungiyar ta dauko aron wani dan wasan gaba daga kungiyar Alraed, Alghamedi, wanda zai maye gurbin Ahmed Musa har zuwa karshen kakar wasanni ta bana.