✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ahmed Musa zai buga wasan farko a Kano Pillars

Ahmed Musa zai buga mata wasan farko tun bayan komawarsa kungiyar a watan Afrilu.

Sabon dan wasan Kano Pillars, Ahmed Musa, zai haska a wasan farko dai zai buga wa kungiyar yayin haduwar da za ta yi da Adamawa United a ranar Lahadi, 16 ga watan Mayu, a gasar Firimiyar Najeriya.

Pillars ta sanar da cewa Ahmed Musa wanda ke zaman kyaftin din tawagar kwallon kafar Najeriya, zai buga mata wasan farko tun bayan komawarsa kungiyar a watan Afrilun da ya gabata.

Tun a watan Oktoban bara ce Ahmed Musa ya rabu da kungiyar Al Nassr FC bayan shekaru biyu yana fafatawa a gasar kwallon kafa ta Kasar Saudiyya.

Ana iya tuna cewa, a ranar Litinin, 19 ga watan Afrilun 2021 ne sabon dan wasan ya fara atisaye da Kano Pillarsa a barikin Bukabu da ke birnin Kano, inda masharhanta ke cewa ya daga darajar kungiyar da ake yi wa lakabi da “Masu Gida”.

A yanzu haka dai Pillars ita ce ta biyu a gasar Firimiyar Najeriya da maki 37 daidai da Akwa United da ke saman teburin bayan buga wasanni 20.