✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin alherin Ambasada Gwani ya sosa wa al’ummar Agangaro rai

Mafi yawan al'ummar da ke rayuwa a garin Fulani ne.

Garin Agangaro gari ne dake kusa da Rafi a yankin Gwani na Karamara Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe da ke da nisan kilomita 80 daga Gombe da bai da hanyar mota ba asibiti ba makaranta, daga garin Gwani zuwa Agangaro awa guda ne saboda rashin hanya.

Al’ummar garin mafi yawan su Fulani ne sai daidaiku Hausawa da Terawa kuma garin mahada ne na kauyuka daban daban da suke da yawan jama’ar da basu gaza dubu 2000,ba suna fama da matasalar rayuwa ‘ya’yan su basa makaranta wanda hakan tasa tsohon Jakadan Najeriya a kasar Cuba Amabsada Ibrahim Habu Gwani ya gina musu firamare mai azuzuwan karatu biyu da ofishin malamai.

A lokacin bikin bude wannan makaranta wacce gwamnatin jihar Gombe ta karba mu’assasin wannan makaranta Ambasada Ibrahim Habu Gwani, yace ya gina makarantar ne domin taimakawa ‘ya’yan Fulani wajen samun ilimin zamani dan suma su kara fahimtar rayuwa.

Gwani, yace wannan gari na Agangaro, yafi shekara 100 da kafuwa kuma mahada ne na wasu kauyuka dake kewaye da garin amma basu da makaranta basu da asibiti basu da ruwan sha, inda yace ya yi ne dan ya jawo hankalin gwamnati ta tuna da yankin.

A cewar sa kafin ya gina wannan makarantar da a gindin bishiya suke karatu irin na yaki da jahilci wanda al’ummar garin suke daukar nauyin bai wa malaman da suke koyar da Yaran nasu dan abun hasafi da filin Noma dan karfafa musu guiwar karantar da Yaran su.

Daga nan sai ya yabawa kokarin gwamnati na shigowa da tayi ta karbi makarantar ta zama ta gwamnati daga makarantar al’umma inda ya kiraye su da su inganta makarantar.

Da take tsokaci kan kokarin Ambasadan Farfesa Halima Abba, daga jami’a mallakar jihar Gombe wacce yar asalin garin Gwani ce tace ita ma za ta bada nata gudumawar muddin tana raye wajen ganin ta dauki nauyin karatun wasu Yaran a makarantun gaba da Firamare

A nasa Jami’in hukumar samar da ilimi na bai daya SUBEB Sani Sabo, yace tunda gwamnati ta karbi makarantar za ta yi duk abunda ya dace inda nan take suka bada gudumawar takardun karatu da kayayyakin aiki.

Da yake nasa tsokaci shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Gwani Alhaji Ibrahim Dauda, cewa ya yi wannan abun alkahir da Ambasada ya yi musu suma nan gaba za su saka masa domin ya ceto wannan al’umma daga duhun jahilci.

Alhaji Ibrahim sai ya kirayi gwamnati da ta hade wannan yankin zuwa garin Gwani da hanya sannan ta samar musu da ruwan sha da kuma asibiti da sauran abubuwan more rayuwa.

Shi ma Dagacin garin na Agangaro, Alhaji Tukur Adamu jinjinawa Ambasada Gwani ya yi bisa gina musu wannan makaranta tare da yiwa ‘Ya’yan su rijistar shiga makarantar kyauta.

Wasu ‘Ya’yan Fulani da suke makarantar da muka zanta dasu sun bayyana farin cikin su da cewa suma yanzu sun samu hanyar yin ilimin zamani wanda zai sa suyi gogaggaya da Yaran birni.