✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin Hajj: NAHCON ta fadada Tsarin Adashin Gata

Adashin gatan kujerar aikin Hajji na dab da karade Najeriya

Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta fadada tsarinta na adashin gatan maniyyata aikin Hajji a kasar.

A ranar 4 ga watan Oktoba NAHCON ta kaddamar da shirin a Jihar Kano, don ba wa maniyyata damar tara kudade a hankali-hankali na tsawon lokacin domin biyan kudin kujerar aikin Hajji.

NAHCON ce ta kirkiro da Tsarin Adashin Gatan Aikin Hajji (HSS) ne da hadin gwiwar Hukumomin Kula da Jin Dadin Alhazai na jihoihi da kuma Bankin Jaiz.

Ana fatar tsarin zai taimaka wajen rage tsadar kujerar aikin Hajji, ya saukaka harkar jigilar alhazai baya ga sauran alfanon da zai samar.

HSS na ba da gurbi ga maniyyata na gwargwadon lokacin suka biya kudi, wato farkon biya, farkon samun kujera.

Masu bukata na shiga tsarin ne ta hanyar yin rajista da hukumomin alhazan jihohinsu wadanda su kuma za su bude musu asusun ajiya a bankin.

A ranar Litinin 15 ga watan Disamba NAHCON za ta kaddamar da shirin a birnin Osogbo na Jihar Osun domin maniyyata daga yankin Kudu maso su amfana.

Washegari kuma za a kaddamar da shirin a garin Ado Ekiti na Jihar Ekiti da kuma Akure na Jihar Ondo sannan a yi na Jihar Legas a ranar 17 ga wata.

Sanarwar fadada shirin adashin gatan zuwa yankin Kudu maso Yamma ta ce kungiyoyin Musulunci, da attajiyar a bangare aikin Hajji za su halarci taron.