✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin Hajji: Saudiyya ta karbi rukunin farko na maniyyatan bana

Mahukuntan Saudiyya sun karbi maniyyata 358 daga kasar Indonesia da dabino da furanni.

Saudiyya ta karbi rukunin farko na maniyyatan aikin Hajji daga wata kasa tun bayan barkewar annobar Coronavirus a watan Maris na 2020.

Kafar Yada Labaran da suka shafi Masallatan Harami ta Haramain Sharifai, ta ruwaito cewa mahukuntan Saudiyya sun karbi maniyyata 358 daga kasar Indonesia da dabino da furanni.

A shekaru biyu da suka gabata an rage yawan maniyyatan da za su shiga birnin Makkah, amma a Yulin bana Musulmi daga sassan duniya za su yi aikin Hajji – daya daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar.

Aminiya ta ruwaito cewa, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Najeriya NAHCON ta ce masu son zuwa aikin Hajji na shekarar 2022 za su biya kusan naira miliyan biyu da rabi.

A cewar hukumar, mazauna yankin Arewacin Najeriya za su biya jimillar kudi naira 2,449,607.89, yayin da na yankin Kudu za su biya 2,496,815.29.

Mazauna jihohin Borno da Yola kuma za su biya 2,408,197.89, a cewar hukumar.

Haka kuma Hukumar NAHCON ta sanar cewa za a soma jigilar maniyyatan daga Najeriya a ranar Alhamis 9 ga watan Yuni, 2022.

Hajji dai wajibi ne ga duk musulmin da yake da hali – akalla sau daya a rayuwarsa.