✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abun da ya kai Buhari Landan a wannan karon

Zai halarci taron ilimi na duniya da kuma tattaunawar hadin guiwa da wasu kasashe.

Shugaban Buhari ya isa birnin Landan na kasar Burtaniya, domin halartar babban taron Ilimi Kan Samar da Kudade ga Kawancen Ilimi na Duniya (GPE) daga shekarar 2021 zuwa 2025.

Firayim Ministan Burtaniya, Boris Johnson, da Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta ne za su dauki nauyin taron da fatar bunkasa ilimi a kasashe kimanin 90, ciki har da Najeriya a nan gaba.

Taron na Landan zai hada shugabannin kasashe da na gwamnatoci da gami da masu ruwa da tsaki da shugabannin matasa, da zummar bullo da hanyoyin da za a bi wajen sauya tsarin ilimi a kasashen kawancen ta hanyar musayar fikira.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban, Femi Adesina ya yi a baya ta ce, “Hakanan zai ba da dama ga shugabanni su yi alkawura na shekara 5 don tallafa wa aikin GPE wajen sauya tsarin ilimi a kasashe da yankuna 90.

“Bututwan da Babban Taron zai tattauna sun hada da : ‘Karfin Ilimi –Tattaunawa Tsakanin Zakarun Duniya’; ‘Sauyin Ilimin ’Ya’ya Mata’; ‘‘Samar da Kudade domin Tabbatar da Tasiri da Farfadowa’; da kuma ‘Mene ne abin yi Yanzu? Muhimman Abubuwan Kawo Sauyin Ilimi a Shekara Biyar Masu Zuwa’, da sauransu,” a cewar Adesina.

Ya ce shugaban na Najeriya zai kuma yi ganawar hadin guiwa da Firayim Ministan Burtaniya.

Bayan kammala taron, Buhari zai kwashe wasu kwanaki domin gainin likitansa a Landan, daga nan “zai dawo a Najeriya mako na biyu na watan Agusta 2021.”