✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aisha Buhari ba ta ce komai kan Daliban Kanakara ba

Mako daya da sace daliban Kankara, Matar Shugaban Kasa ba ta yi magana a kai ba

A yayin da duniya ke kara juyayi da kiraye-kirayen a ceto daliban da aka yi garkuwa da su a jihar Shugaba Buhari ta Katsina, har yanzu matarsa Aisha ba ta yi magana a kan batun ba.

Mako guda ke nan da ’yan bindiga suka sace daliban a makarantar kwana ta Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (GSSS) da ke garin Kankara a jihar mijinta, amma ba a ji ta ce komai a kai ba.

Hankula sun kara tashi a ranar Alhamis game da halin da yaran ke ke ciki bayan kungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyonsu suna rokon gwamnati ta ceci rayuwarsu, kwana shida bayan ta yi awon gaba da su.

Rashin tsokacin Aisha Buhari kan sace yaran ya saba da yadda aka san ta da  nuna alhini da neman gwamnati ta yi abin da ya dace a kan abubuwan da ke damun jama’ar Najeriya.

Yadda take tsokaci akan lamurra ya sa wasu ke yabawa da yadda take nuna damuwa kan halin da al’umma ke ci, har ake daukar ta a matsayin abar koyi.

Sai dai har zuwa daren ranar Alhamis ba a ji ta yi magana ko fitar da sanarwa ta hannun hadimanta game yin garkuwa da daliban ba, abin da ya zo da ban mamaki.

Babban motsin Aisha Buhari da aka ji na karshe-karshe a shafukan zumunta shi ne sakon da ta wallafa kan neman kawo karshen matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

Ta wallafa wani sako da ta yi amfani da maudu’an #Acecjama’a a ranar 17 ga watan Oktoba wanda ta sanya hoton Shugaba Buhari da manyan Hafsoshin Tsaro suna yi taro.

Washegari kuma ta yi amfani da maudu’in #Arewamufarka inda ta sanya wata wakar rokon Allah da neman agaji ga Buhari kan magance matsalolin da ke addabar Najeriya.

Sakonnin guda biyu da ta wallafa a shafinta na Twitter sun tayar da kura matuka a lokacin.

Ta wallafa su ne a lokacin zanga-zangar #SecureNorth mai kira da ’yan Arewa su farka game da matsalar tsaro da ya addabi yankin.

Hakan ya zo ne a lokacin da matasan yankin suke zanga-zangar da zumman neman gwamnati kawo karshen matsalar tsaro a yankin.

A daidai lokacin kuma ana zanga-zangar #EndSARS a fadin don neman a kawo karshen cin zalin ‘yan sandan rundunar SARS mai yake da ayyukan fashi.

‘Yan bindiga da suka yi musayar wuta da jami’an tsaro masu gadin GSSS Kankara sun yi garkuwa da daliban ne a ranar Juma’a, ‘yan sa’o’i bayan isar Shugaba Buhari mahaifarsa da ke garin Daura, mai tazarar kilomita 200 daga Kankara.

Kungiyar Boko Haram ta ce ita mayakanta ne suka yi garkuwa da daliban makarantar mazan ta kwana, wadanda ta fito da bidiyonsu suna neman Gwamnatin Najeriya ta cece su.

Rashin jin ta bakin Aisha Buhari a kan wannan batu ya sha bamban da yadda ta nuna a game da daliban makarantar Dapchi da ‘yan matan Chibok da sauran mata da masu rauni da suka shiga cikin kangin kaka-ni-ka-yi.