Aisha Buhari ta dawo Najeriya bayan wata shida a Dubai | Aminiya

Aisha Buhari ta dawo Najeriya bayan wata shida a Dubai

Dawowar Aisha Buhari daga Dubai, inda aka duba lafiyarta (Agusta, 2020).
Dawowar Aisha Buhari daga Dubai, inda aka duba lafiyarta (Agusta, 2020).
    Muideen Olaniyi da Sagir Kano Saleh

Matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta dawo Najeriya bayan shafe wata shida a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Aisha Buhari ta shiga Najeria ne a ranar Laraba, bayan ta bar Najeriya ne kwanaki kadan da bikin daurin auren ’yarta Hanan.

Tafiyar da ta yi ta haifar da ce-ce-ku-ce inda wasu ke zargin rashin tsaro a Fadar Shugaban Kasa ce ta sa ta barin kasar.

Sai dai daga baya hadiman Uwar Gidan Shugaban Kasar sun musanta zargin a matsayin shaci-fadi.

Ko kafin daurin Hanan, Aisha Buhari ta jima Dubai inda aka duba lafiyarta, kafin dawowarsu tare da amaryar gab da bikin.