✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aisha Buhari ta janye karar dalibin da ya tsokane ta

Lauyan A'ishah Buhari ya ce ta janye karar ne bayan wasu ’yan Najeriya sun sanya baki.

Matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta janye karar dalibin nan da take zargi da cin mutuncinta a kafofin sada zumunta, Aminu Mohammed.

A ranar Juma’a, lauya mai gabatar da kara, Fidelis Ogbobe ya shaida wa kotun cewa Aisha Buhari ta janye karar ne bayan wasu ’yan Najeriya sun sanya baki.

Tsare dalibin da jami’an tsaro suka yi a makon jiya, kafin daga baya kotu ta tsare shi, ya janyo ce-ce-ku-ce da sukar matar shugaban kasar, gami da kira da a gaggauta sakin shi.

Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito yadda matar shugaban kasar ta rufe shafinta na Twitter a lokacin da aka yi mata ca kan tsare Aminu.