✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aisha Buhari ta tafi Dubai neman magani

Ta dade tana fama da lalura tun bayan dawowarta daga wata ta'aziyya da ta je a Legas

Matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta fice zuwa birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa domin neman magani.

Aminiya ta gano cewa ko a karshen makon jiya sai da Aishan Buhari ta fita zuwa kasar waje saboda ciwon wuya da ya takura mata jim kadan bayan dawowarta Abuja daga Legas.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ta fara fama da ciwon wuyan ne tun kusan lokacin da ta dawo daga ta’aziyyar tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi, wanda cutar coronavirus ta yi ajalinsa.

Aisha dai ta killace kanta na tsawon makonni biyu bayan ciwon wuyan nata ya ki ci ya ki cinyewa kusan wata daya da zuwa ta’aziyyar a Legas.

Hakan ne ya tilasta mata yanke shawarar zuwa Dubai din don neman kulawar gaggawa.

Aminiya ta gano cewa yanzu haka tana can a wani asibitin da ba a bayyana ba, kuma tana murmurewa.

Sai dai da aka tuntube shi ta wayar salula, Mai Taimaka wa Shugaban Kasa ta Bangaren Watsa Labarai a Ofishin Matar Shugaban Kasa, Barista Aliyu Abdullahi ya ki cewa uffan a kan lamarin.

Ya ce, “Na yi tafiya, ba na ofis tsawon makonni biyu, don haka ba zan iya cewa komai ba”.