✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ajantina ta lallasa Croatia da ci uku da nema

Kasar Ajantina ta lallasa Croatia da ci uku da nema domin kai wa ga wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya da ake buqagawa a…

Kasar Ajantina ta lallasa Croatia da ci uku da nema domin kai wa ga wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya da ake buqagawa a Qatar.

Messi ne ya fara jefa kwallo a ragar Croatia a bugun fanareti a minti 34 da fara wasa, sannan dan wasan gaba, Julián Álvarez ya zura na biyu a minti 39, sannan ya kara a minti 69.

Yanzu Ajantina za ta jira wasan gobe da za a fafata tsakanin Maroko da Faransa ne domin kasar da za ta fafata da ita a wasan karshe.

Domin karanta yadda ta kaya a wasan, a shiga kai-tsaye a kasa: