✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akasarin titunan Najeriya sun mutu murus – FERMA

Shugaban hukumar ne ya bayyana hakan a Kaduna

Hukumar Kula da Gyaran Tituna ta Tarayya (FERMA), ta gargadi masu ababen hawa a Najeriya da su rika tuki da lura saboda galibin titunan kasar sun mutu murus.

Shugaban hukumar, Nurudeen Rafindadi ne ya yi gargadin lokacin da yake jawabi yayin bikin lakca da bayar da kyaututtuka na Kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya (NSE) reshen jihar Kaduna karo na 10 a karshen mako.

Shugaban na FERMA wasu daga cikin manyan hanyoyin kasar nan an gina su ne don kada su wuce shekara 15 zuwa 20, amma yanzu sun haura shekara 50.

A cewarta, “Yawancin manyan titunan Najeriya sun mutu. Abin da muke kokarin yi a yanzu shi ne yin tattalin hanyoyin da suka riga suka lalace, wadanda aka gina su don kada su wuce shekara 15 zuwa 20, ko idan sun yi tsanani, shekara 25, amma yanzu muna da hanyoyin da aka shekara 50 da gina su,” inji shi.

Nuruddeen, wanda a taron ya sami wakilicin Shugaban FERMA na Kaduna, Atiku Sadiq, ya yi magana ne a kan makala mai taken, “Kalubale da damarmakin da ke tattare da amfani da manyan hanyoyin Najeriya.”

Daga nan sai ya bayar da shawarar cewa babbar hanyar da za a yi amfani da ita wajen ci gaba da tabbatar da lafiyar titunan ita ce ta yawan yi musu gyara a kai a kai.

Shi kuwa shugaban NSE reshen jihar ta Kaduna, Abubakar Jumare, ya ce taken taron na bana, “Muhimman abubuwan da ke ci wa harkar sufuri tuwo a kwarya” an zabe shi ne an zabe shi ne domin a magance tarin kalubalen da manyan hanyoyin Najeriya ke fuskanta.