✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akon zai gina sabon birni don maido da ’yan Afirka mazauna Turai gida

Shahararren mawakin duniya, Alioune Badara Thiam wanda aka fi sani da Akon, dan asalin kasar Senegal mazaunin Amurka, ya kudiri aniyar gina sabon birni a kasarsa…

Shahararren mawakin duniya, Alioune Badara Thiam wanda aka fi sani da Akon, dan asalin kasar Senegal mazaunin Amurka, ya kudiri aniyar gina sabon birni a kasarsa ta asali domin jan hankalin yan Afirka mazauna kasashen Turai su rika komawa gida.

Zai gina katafaren birnin ne a Kudu da Dakar babban birnin Senegal, kuma aikin zai lashe zunzurutun kudi Dalar Amurka biliyan shida.

A ranar Litinin 31 ga watan Agusta, tauraron na R&B wanda ya kaddamar da sabbin album biyu na wakokinsa ya fada wa ’yan jarida cewa ya aza harsashin ginin sabon birnin da ke daura da tekun Mbodiene mai nisan kilomita 100 daga Dakar.

Akon ya ce ya taso a garin New Jersey na kasar Amurka bayan da danginsa suka koma can da zama a lokacin yana dan shekara bakwai.

“Na yi cudanya da ’yan asalin Afirka mazauna Amurka da dama wadanda ba su san al’adunsu ba; yawancinsu sun mance da asalinsu.

“Don haka nake son dabbaka aiki ko birnin da zai sauya masu tunani, domin su san asalinsu su fahimci cewa suna da gidajensu na gado bayan wadanda suke a yanzu kuma ina samun kwarin gwiwa daga shugabannin yankin Mbodiene”, inji Akon.

Ya ce za a kawata birnin na Akon da gidajen baki da jami’a da cibiyar kula da lafiya da cibiyoyin kasuwanci da wuraren shakatawa na musamman da manyan cibiyoyin hada finafinai da wakoki hade da kayatattun studiyo dominsu.

“Aikin da shahararren mai zayyanar birane na Afirka Hussein Bakri zai jagoranta zai kawata birnin da tsarin al’adun gargajiyar kasashen Afrika.

“Birnin Akon zai samar da kauyuka na al’adun Afirka ta yadda duk  wanda ya zo daga Amurka ko Birtaniya, ko ma dai ina ne daga Turai babu inda zai so ya fara sa kafa a Afirka sai Sanegal.

“Muna so Sanegal ta zama zango na farko ga duk wanda yake so ya ziyarci nahiyar Afirka”, inji mawakin.