✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Akwai alamun ASUU za ta janye yajin aiki

Gwamnatin tarayya ta amince zata jiya ASUU 70bn don biyan alawus-alawus.

Alamu na  nuna yiwuwar Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta janye yajin aikin da take yi na tsawom wata tara, bayan gwamnati ta amince da biyan wasu daga cikin bukatunsu.

A karshen zaman kungiyar da bangaren gwamnati a ranar Juma’a, gwamnatin ta amince da ware Naira biliyan 70 domin biyan alawus da malaman ke bin ta da kuma wasu bukatu.

Bangaren gwamnatin ya ce kudaden sun hada da Naira biliyan 40 na alawus din malaman da kuma Naira biliyan 30 na gyaran tsarin karatu.

Gwamnatin ta kuma yi alkawarin biyan albashin malaman da suke bi tun daga watan Fabrairu 2020, kafin ranar 31 ga Disamba, 2020.

A satin da ya gabata, Aminiya ta ruwaito cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da cire ASUU daga tsarin biyan albashi na IPPIS na dan lokaci.

Da yake tattaunawa da menama labarai, Ministan Kwadago da Daukar Ayyuka, Chris Ngige, ya ce ana sa ran taron zai haifar da da mai ido.

Da aka yi wa Shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi tambaya, sai ya ce duk abin da Ministan ya fada wa manema labarai gaskiya ne.

Ana san ran a zama na gaba dukkanin bangarorin za su amince tare da kawo karshen yajin aikin.