✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin akwai bambanci tsakanin Buhari da Osinbajo?

Babbar tambayar da ’yan Najeriya ke yi ita ce ko akwai banbanci tsakanin Buhari da Osinbajo?

Kawo yanzu ta tabbata cewa Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bi sahun sauran masu zawarcin mulkin Najeriya a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

A ranar Litin ce Osinbajo ya bayyana kudurinsa na neman takarar Shugaban Kasa a babban zabe mai zuwa domin zama magajin Shugaba Muhammadu Buhari wajen ci gaba da rike Najeriya.

Mataimakin Shugaban Kasar ya bayyana aniyar takarar tasa ce kwanaki 89 bayan da ubangidansa a siyasance, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shi ma ya bayyana kudurinsa na neman tsayawa takarar kujerar.

Sai dai tambayar da take ta kai komo a labban ’yan Najeriya ita ce, ko salon mulkinsa zai bambanta da na Buharin, wanda duk wainar gwamnatin da shi aka toya a matsayin Mataimaki na kusan shekara takwas?

A lokacin da yake ayyana takarar tasa cikin wani bidiyo da aka yada ta shafukansa na sada zumunta, Osinbajo ya bayyana irin ayyukan da zai yi wa kasa idan ya gaji Shugaba Buhari.

A cikin jawabin nasa, an ji shi yana cewa, “Tare da kankan da kai, a yau ina mai bayyana kudirina na neman ofishin shugaban kasar Tarayya Najeriya a hukumance karkashin inuwar jam’iyyar APC.”

Ya ce idan ya samu wannan dama, a shirye yake ya dora daga inda Shugaba Buhari ya tsaya.

Osinbajo, ya kuma ce zai gyara harkar tsaro da kuma kammala garambawul ga bangaren shari’a, kula da walwalar ma’aikatan shari’a domin tabbatar da an yi wa kowa adalci da sauransu.

Babban abin jira a gani a yanzu dai shi ne ko Osinbajo zai iya kai bantensa yayin zaben fid da gwanin jam’iyyar wanda za a yi ba watan Mayu mai zuwa.