✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai barazanar kisa da garkuwa da ’yan Majalisar Dokoki ta Tarayya —DSS

A karon farko DSS ta ambaci ’yan Majalisar Tarayya kai-tsaye a jerin mutanen da ke cikin hadarin garkuwa da su

Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta sanar cewa ’yan Majalisar Dokoki ta Tarayya suna fuskantar barazanar kisa ko garkuwa da su domin karbar kudaden fansa.

DSS ta bayyana hakan ne a daidai lokacin da ’yan majalisar da sauran ’yan Najeriya ke shirye-shiryen tafiya hutu domin bukukuwan karashen shekara, a yayin da matsalar tsaro ta ki ci, ta ki cinyewa.

“Wadannan mutane suna cikin hadarin kisa, sacewa, garkuwa da su, yi musu fashi, ko suddabarun siyasa,” inji sanarwar da kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ya fitar.

Karon farko ke nan da hukumar ta ambaci ’yan Majalisar Tarayya kai-tsaye a jerin mutanen da ke cikin hadarin garkuwa da su ko yi mu kisan gilla a Najeriya.

A baya hukumar kan yi wa ’yan majalisar kudin goro ne a cikin manyan mutane idan ta tashi fitar da gargadin jerin mutanen da ke cikin hadari ko barazanar tsaro.

A cewar Afunanya, hukumar ta gano shirin bata-gari na amfani da dalibai da za su tafi hutu su shigar da su ayyukan ’yan bindiga da garkuwa da mutane da fashi da tayar da tarzoma da shan miyagun kwayoyi da sauran miyagun laifuka.

Afunanya ya ce bata-garin sun riga sun wuce gona da iri, saboda haka ya shawarci “duk masu daukar nauyin wadannan miyagun ayyuka a yankin Arewa ko Kudu, cewa su sake tunani su daina, idan kuma ba haka ba hukumar za ta shafa wa idanunta toka ta murkushe su.”