✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Akwai haramtattun makarantu masu zaman kansu 7,000 a jihar Filato’

Kungiyar Mamallaka makarantu masu zaman kansu ta kasa reshen jihar Filato (APSON), ta ce makarantu 7,000 masu zaman kansu ne ke aiki ba bisa ka’ida…

Kungiyar Mamallaka makarantu masu zaman kansu ta kasa reshen jihar Filato (APSON), ta ce makarantu 7,000 masu zaman kansu ne ke aiki ba bisa ka’ida ba a jihar.

Shugaban kungiyar, Mista Solomon Musa, ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, in da ya ce yunkurin Gwamnatin na sabunta lasisin dukkanin makarantun abu  ne mai kyau da zai kawo karshen haramtattun makarantun.

Ya kuma ce bayyana hakan a matsayin wani abu da ke durkusar da ci gaban ilimin jihar.

“Maganar da na ke muku yanzu haka makarantun nan ba su da takardun izinin gudanarwa na gwamnati, kuma duk da muna yaba wa kokarin gwamnati, amma lamarin sai ta dada jajircewa.

“Mutanen nan saboda sun san ba bisa ka’ida suka bude makarantun ba, shi ya sa ma ba su yi yunkurin shiga kungiyarmu ta APSON ba.

“A matsayinmu na kungiya, muna goyon bayanta 100 bisa 100, don ba  a wasa da harkar Ilimi,” inji shi.

Shugaban ya kuma shawarci mambobin kungiyar ta su da su yi biyayya ga umarnin gwamnatin jihar na sabun rajistar makarantunsu don gudun abin da ka je ya zo.