✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Akwai masu yi min zagon kasa a mulkina – Wike

Gwamnan ya ce masu yin hakan na kokarin ja ne da ikon Allah.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom ya ce rikicin baya-bayan nan da ake samu a jam’iyyar PDP yana samun goyon bayan wadanda ya bayyana a matsayin masu yi masa zagon kasa don ganin sun durkusar da gwamnatinsa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen bikin godiya da Alkalin Alkalilan Jihar, Mai Shari’a Simon Amadi ya shirya a Elibrada da ke karamar hukumar Emohua ta jihar a karshen satin da ya gabata.

Gwamnan ya ce duk masu shirya  makarkashiya ga gwamnatin tasa hakarsu ba zata cimma ruwa ba.

Wike, wanda ya bayyana mamakinsa kan mutanen, ya kuma ce babu wanda zai iya ja da ikon Allah, domin Allah ne ya kaddari ya zama Gwamnan Jihar.

Da yake nasa jawabin, Mai Shari’a Simeon Chibuzor Amadi ya ce Allah ne kadai ya cancanci a yi masa godiya bisa yadda ya kyautata rayuwar sa, da kuma nadinsa a matsayin Alkalin Alkalai.

A karshe kuma ya yi kira da al’ummar Jihar da su kasance masu godiya da irin yadda gwamnatin ke kokorin kawo ci gaban Jihar a kodayaushe.