✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai tserarrun fursunoni 3,906 da muke nema ruwa a jallo – Aregbesola

“Za mu ci gaba da jira komai daren dadewa, ba za su iya buya ba.”

Ministan Al’amuran Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya ce har yanzu akwai fursunoni kimanin 3,906 da suka cika wandonsu da iska daga gidajen gyaran hali daban-daban na Najeriya kuma suka ki dawowa.

Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, lokacin da yake jawabi ga manema labarai a wani taro da ayarin jami’an yada labaran Shugaban Kasa suka shirya fadar Shugaban da ke Abuja.

A cewar Ministan, daga shekarar 2020 zuwa yau, akalla fursunoni 4,369 ne suka tsere daga gidajen kurkuku, Amma 984 ne kawai aka sami nasarar cafkewa daga cikinsu.

Aregbesola ya ce tuni an riga an dauki zanen yatsun dukkan fursunonin, inda ya ce hakan zai taimaka wajen ganowa tare da sake cafke su, da hadin gwiwar ’yan sandan kasa da kasa na Interpol.

Ya ce, “Har iya tsawon wannne lokaci za su iya tsere mana? Za mu ci gaba da jira komai daren dadewa. Za su iya guduwa, amma ba za su iya buya ba.

“Muna da zanen yatsunsu, duk lokacin da suka yi kokarin yin kowacce irin huldar kasuwanci, ko a ina ne, asirinsu zai tonu,” inji Aregbesola.

Ministan ya kuma ce yanzu haka, akwai fursunoni 465 da ke karatun digiri a fannoni daban-daban a fadin kasar nan, 81 kuma na yin digiri na biyu, hudu kuma na karatun digirin digirgir.

Kazalika, ya ce akwai fursunoni 560 da suka yi rajistar jarabawar NECO da WAEC, 2,300 kuma suke ilimin yaki da jahilci a gidajen gyaran hali daban-daban na Najeriya.