✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai ’yan Boko Haram 61,000 tsare a gidajen yarin Arewa maso Gabas – Aregbesola

Ya kuma ja kunnen masu gadin gidajen gyaran hali

Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya ce akwai mayakan Boko Haram akalla 61,000 da ke tsare a gidajen yarin Jihohin Arewa maso Gabas.

Ministan ya kuma ja kunnen jami’an tsaron Najeriya da ke gadin gidajen gyaran halin da su kasance cikin shiri a kodayaushe domin dakile harin ’yan ta’adda.

Aregbesola ya yi wannan jan kunnen ne ranar Talata, lokacin da ya kai ziyara gidan gyaran hali na Kirikiri da ke Apapan jihar Legas.

Cikin wata sanarwa da mataimakinsa, Sola Fasure, ya raba wa manema labarai, Aregbesola ya ce, “Wannan jan hankalin ya zamo dole kasancewar muna lalubo sabbin dabarun dakile hare-hare cikin hikima ba tare da wani tsoro ba.

“Na kuma sanar da jami’anmu da muatnen da ke wannan guri, kan dole ne su yi yaki don kare hukumominmu, yankunanmu da kundin tsarin mulkinmu.

“Hakan kuma ya shafi duk sauran jami’an tsaron da ke saura sassan Najeriya.

“Kar a kyale wasu kungiyoyin ’yan ku-ci-ku-ba-mu su dinga kai hari kan hukumominmu su na kuma tserewa ba tare da mun yi galaba a kan su ba. Ya zamo dole a hana su kai labari.”

Kazalika, ya ce fiye da fursunoni 800 ne ciki har da 64 da ake zargin ’yan Boko Haram ne, suka tsere a harin da wasu ’yan bindiga suka kai gidan yarin Kuje makon da ya gabata.

Sai dai ministan ya ce kasar nan na kan hanyar murkushe ’yan ta’addan Boko Haram gaba daya, da ma sauran miyagun da ke addabar ta, inda ya ce an kama da yawa daga cikinsu musamman a yankin Arewa maso Gabas.

“A yau, jiga-jigan masu aikata laifuka da masu tayar da kayar baya a fadin kasar nan muna kan hanyar murkushe su mun wulakanta su, kuma sama da 61,000 daga cikinsu na tsare a Arewa maso Gabas.

“Tabbacinmu ga ’yan Najeriya shi ne za mu yi nasara kan wadannan kalubalen, kuma mu fito da kwarinmu fiye da yadda aka same mu ma a baya,” inji Ministan.

A bangaren hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya kuwa, Ministan ya ce ya kamata su inganta kokarin da suke yi na tattara bayanan sirri da kuma yin aiki da su, domin hakan ne a cewarsa zai magance matsalar hare-haren da ake kaiwa cibiyoyin.

“Ya zuwa yanzu, babu wani tserewa daga gidan yari da fursunonin suka samu nasarar yi, duk mun murkushe su gaba daya. Abin da muke samu tun zanga-zangar #EndSARS ta watan Oktoban 2020, shi ne yadda mutane ke kawo hari don tserar da mutanensa da ke tsare a wurinmu,” a cewarsa.