✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Akwai ’yan kabilar Kanuri sama da miliyan 2 a Kano’

Mai Mustapha Lawan ya ce bayan Hausawa babu ’yan kabilar da suka fi Kanuri yawa a Jihar Kano

Basaraken ’yan kabilar Kanuri mazauna Kano, wato Mai Kanuribe, Mai Mustapha Lawan, ya ce akwai ’yan kabilarsu sama da mutum miliyan biyu a fadin jihar Kano.

Hakan, a cewarsa ya sa bayan Hausawa wadanda su ne suka fi yawa a jihar, babu ’yan wata kabila da ta fi tasu yawa a jihar.

Ya bayyana hakan ne a Kano ranar Lahadi, yayin bikin nadin wasu sarautun gargajiya daga kananan hukumomin jihar 44 da ya yi.

Mai Kanuribe, ya ce sabbin mutanen da aka nada din su ne za su kasance a matsayin jakadunsa a fadin jihar, kamar yadda shi ma yake zama wakilin Shehun Borno a Kano.

Ya ce, “Akwai mutanenmu masu dimbin yawa a nan Kano, mun haura miliyan bisa ga kididdigar da muke da ita. Mu ne kabila ta biyu mafi yawa a Kano bayan Hausawa.

“Wadannan sababbin sarautun da muka bayar za su samar da wani cikakken tsari; A baya kawai kowa zaman kansa yake yi.

“Babban burinmu shi ne a nan gaba, duk wanda ya zo daga yankinmu, muna so mu san da zamansa; Ko da gida zai saya ko ya gina, muna so mu rika sani.

“A yau, na nada sama da mutum 40 sarauta a fadin jihar nan,” inji basaraken.

Sai dai ya yi kira ga sabbin wadanda aka nada din da su kasance jakadu na gari da za su taimaka wajen hadin kan jama’a da kawo wa jihar ci gaba.

Mai Mustapha ya kuma bukace su da su yi aiki tukuru wajen magance matsalolin jama’arsu a yankunansu.

Idan za a iya tunawa, a bara ne dai Shehun Borno ya nada Mai Mustapha Lawan a matsayin Mai Kanuribe na Kano, kuma jakadan masarautar a jihar.