✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai ’yan kwaya miliyan 2 a Kano – Shugaban NDLEA

Hakan na nuna cewa a cikin duk mutum shida a Jihar, daya dan kwaya ne.

Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya ce akwai masu ta’ammali da miyagun kwayoyi kimanin miliyan biyu a Jihar Kano.

Ya bayyana hakan ne a Kano ranar Litinin lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje a Gidan Gwamnatin Jihar.

Buba Marwa ya ce, “A Jihar Kano, ta’ammali da miyagun kwayoyi ya kai kimanin kaso 16 cikin 100; ma’ana a cikin duk mutum shida, daya dan kwaya ne, kuma alkaluman sun kunshi ’yan tsakanin shekara 15 zuwa 65 a duniya.

“Akwai kimanin mutum miliyan biyu masu ta’ammali da kwayoyin da suka hada da Kodin, da Tramadol da sauran magungunan tari da kuma Tabar Wiwi.

“Amma tun da na karbi ragamar shugabancin hukumar NDLEA a watan Janairu, mun kwace sama da kilogiram miliyan biyu na miyagun kwayoyi da kimarsu ta kai ta biliyoyin Nairori.

“Ta’ammali da miyagun kwayoyi ya kai wani yanayin da yake lalata tarbiyya ya kuma tarwatsa iyalai. Ya zama wajibi mu tashi tsaye mu yaki wannan dabi’ar,” inji shi.

Buba Marwa ya kuma ce karuwar ayyukan ta’addanci na da nasaba da karuwar aikata laifuka kamar su satar mutane, fashi da makami, ta’addanci da dai sauransu.

Shugaban wanda kuma ya ce ya gamsu da rawar da Gwamnatin Jihar take takawa wajen yaki da dabi’ar, ya kuma ba da shawarar kafa dokar da za ta hana ’yan siyasa ba matasa miyagun kwayoyi.

Kazalika, ya roki Gwamnatin da ta yi dokar da za ta tilasta wa masu son yin aure gwajin miyagun kwayoyin a matsayin wani matakin yaki da ta’ammalin.

Da yake nasa jawabin, Gwamna Ganduje ya ce ana samun yawan masu amfani da kwayoyin ne a Jihar sakamakon ita ce ta fi kowacce yawan jama’a da kuma kasancewarta cibiyar kasuwanci.

Ya ce hakan ne ya ke jefa ta cikin tsaka mai wuya saboda ta kowacce hanya a kan shigo mata da kwayoyin.

Ganduje ya ce tuni Jihar ta kafa dokar tilasta yi wa Kwamishinoni da Manyan Sakatarorin gwamnati gwaji kafin a nada su a kan mukami da nufin magance matsalar.