✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Akwai ’yan majalisa da dama masu goyon bayan yunkurin tsige Buhari’

Sanatan ya ce masu son tsigewar suna da yawa

Sanatan APC mai wakiltar Bauchi ta Arewa a Majalisar Dattawa, Adamu Bulkachuwa, ya ce akwai takwarorinsa da dama da ke goyon bayan yunkurin tsige Muhammadu Buhari daga shugabancin Najeriya.

A makon da ya gabata ne dai kusoshin jam’iyyar adawa ta PDP a majalisar suka ba Buharin wa’adin mako shida ya kawo karshen matsalar tsaro ko su tsige shi.

Sai dai yayin wata hirarsa da gidan talabijin na Channels ranar Litinin, Sanatan ya ce batun tsigewar kusan shi ne abu na karshe da ya rage wa ’yan majalisar.

Ya ce shi da sauran tawarorinsa sun sha yunkurin taimaka wa bangaren zartarwa da ma Shugaban Kasa kan magance matsalar tsaron amma lamarin ya ci tura.

Dan majalisar ya ce, “Lokacin da muka fahimci cewa kusan duk abin da aka yi bai yi aiki ba kuma sha’anin tsaro har ma da tattalin arziki na dada tabarbarewa, sai muka fahimci cewa mu kawai wani bangare ne na gwamnati da ba shi da ikon zartarwa.

“Abin kawai da za mu iya yi shi ne mu jawo hankalin bangaren zartarwa, kuma mun yi kusan duk abin da za mu iya amma babu wani sakamako, watakila barazanar tsigewar ce kawai za ta sa su yi abin da ya dace,” inji Sanata Bulkachuwa.

Kalaman na Sanatan na APC na zuwa ne kusan kwana biyar bayan Sanatocin jam’iyyar adawa, akasarinsu ’yan PDP sun fice daga zauren majalisar don nuna bacin ransu kan tabarbarewar sha’anin tsaro a Najeriya.

Ficewa daga majalisar ta biyo bayan matakin da Shugaban majalisar, Sanata Ahmed Lawan ya dauka na yin watsi da tattauna batun matsalar tsaro da kuma yunkurin tsige buharin, wanda Shugaban Marasa Rinjaye na majalisar, Sanata Philip Aduda ya jagoranta.