✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai ’yan Najeriya 322,000 da ke gudun hijira a makwabtan kasashe – Minista

Ta ce an fara shirye-shiryen yadda za a dawo da su gida.

Ministar Jin-kai da Agajin Gaggawa, Hajiya Sadiya Umar-Farouk ta ce akwai ’yan Najeriya kimanin 322,00 da yanzu haka suke gudun hijira a makwabtan kasashe.

Ta bayyana hakan ne ranar Asabar a Abuja yayin mika ragamar shugabancin wani kwamiti ga Kwamishiniyar Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira, Gajiyayyu da Wadanda Yaki ya Daidaita ta Kasa (NCFRMI), Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim.

An dai gudanar da bikin mika ragamar kwamitin ne wanda aka dora wa alhakin dawo da ’yan Najeriya gida daga kasashen Nijar da Kamaru da Chadi a Cibiyar Sojojin Kasa da ke Abuja.

A cewar Ministar, daga cikin adadin, mutum 186,957 suna Jamhuriyar Nijar, 118,409 na kasar Kamaru sai kuma 16,634 da ke kasar Chadi.

Hajiya Sadiya ta ce la’akari da karuwar yawan ’yan gudun hijirar a kasashen ya sa gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa a hukumance da kasahen Chadi da Nijar, kuma ta sa hannu a makamanciyar wannan yarjejeniyar da kasar Kamaru.

Ita ma da take jawabi, Kwamishiniyar NCFRMI, Hajiya Imaan ta ce an dora wa kwamitin alhakin tabbatar da an dawo da mutanen gida cikin kwanciyar hankali, kamar yadda Ma’aikatar Jin-kan ta bukata.