✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Akwai yiwuwar a sami karancin fita kada kuri’a a 2023 daga Arewa’

CNG ta ce hakan ba ya rasa nasaba da kamun ludayin Buhari

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar a sami karancin masu fita kada kuri’a a babban zaben 2023 mai zuwa daga Arewacin Najeriya.

Da yake jawabi ga manema labarai ranar Litinin a Kano, Kakakin kungiyar, Abdulaziz Suleiman, ya ce bincikensu ya gano cewa ana samun karancin masu fita su sabunta katin zabensu a yankin, musamman idan aka kwatanta da sauran sassan kasar.

A cewar CNG, hakan ba ya rasa nasaba da irin yanke kaunar da mutanen yankin suka yi da salon mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Bugu da kari, kungiyar ta ce salon da aka bi wajen fitar da ’yan takara a manyan jam’iyyun APC da PDP ya dada taimakawa mutanen yankin su nuna halin ko-in-kula da duk ma wanda zai lashe zaben.

Sai dai sun ja hankalin mutanen yankin da kada su yanke kauna kuma su je su karbi katin, saboda shi kadai ne hanyar zabar shugabannin da za su fitar da su daga halin da suka tsinci kansu a ciki.

CNG ta kuma ce kamata ya yi mutanen yankin da ma sauran ’yan Najeriya su yi watsi da jam’iyyu ta hanyar zabar cancanta da gogewa domin kawo wa kasar ci gaba.

Kungiyar ta kuma yi kira da a yi bincike don gano ko amfani da kudin da ake zargi yayin zabukan fitar da gwanin manyan jam’iyyun ya saba da tanade-tanaden Dokar Zabe ta Kasa.