✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Akwai yiwuwar ASUU ta zarce da yajin aikinta har sai abin da hali ya yi’

Kungiyar ta ce har yanzu babu wani abin a-zo-a-gani daga gwamnati

A ranar Lahadi, Kwamitin Zartarwa na Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ya tattauna a Abuja don yanke shawarar ko yajin aikin mako hudun da kungiyar ta tsunduma zai kawo karshe ranar Litinin.

Sai dai wani babban jami’i a kungiyar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce akwai yiwuwar su zarce da yajin aikin har sai abin da hali ya yi, saboda babu wata matsaya da suka samu a tattaunawarsu da gwamnati kan bukatunsu.

Bukatun dai sun hada da fitar da kudaden raya jami’o’in gwamnati da wasu kudaden alawus-alawus na mambobinsu da amincewa da UTAS a matsayin tsarin biyan albashi a maimakon na IPPIS da kuma aiwatar da bukatun yarjejeniyarsu da gwamnati ta shekarar 2009.

Jami’in na ASUU wanda ya halarci tattaunawar ya shaida wa majiyarmu cewa babu wani abin a-zo-a-gani daga gwamnatin har yanzu.

Ya ce, “Muna tattaunawar ne don yanke shawarar ko za mu tsawaita yajin aikin har sai abin da hali ya yi.

“Amma dai abin da ya fi bayyana a zahiri shi ne zamu tafi kawai sai abin da hali ya yi,” inji shi.

Shi kuwa Shugaban ASUU, Emmanuel Victor Osodeke, cewa ya yi, “Babban abin da ke ci mana tuwo a kwarya shi ne wata sanarwa da ta fito daga Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani da kuma Shugaban hukumar NITDA da ke cewa UTAS ya gaza cin gwajin nagarta.

“Idan za a iya tunawa, wannan hukumar ta NITDA da ita ce a ranar 10 ga watan Agustan 2021, a gaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) da sauran hukumomin gwamnati ta ce tsarin ya ci jarabawar,” inji Shugaban na ASUU.

A watan da ya gabata ne dai ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi na mako hudu saboda zargin da ta yi wa Gwamnatin Tarayya na gaza cika alkawuran yarjejeniyoyin da suka kulla da ita a baya.