✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yiwuwar Ronaldo ya sake komawa Real Madrid

Rahotanni dai na ta nuna cewa Cristiano Ronaldo zai iya sauya sheka daga Manchester United zuwa tsohuwar kungiyarsa ta Real Madrid. A watan Agustan bara…

Rahotanni dai na ta nuna cewa Cristiano Ronaldo zai iya sauya sheka daga Manchester United zuwa tsohuwar kungiyarsa ta Real Madrid.

A watan Agustan bara ne Cristiano Ronaldo ya dawo Manchester United daga Juventus ta Italiya wanda daga zuwansa zuwa yanzu, ya ci kwallo 24 a duk wasannin da ya buga a kakar bana.

Sai dai wasu magoya bayan Madrid din suna ganin dawowarsa kungiyar zai iya jefa Mdrid din irin halin da Man United ke ciki.

Hakan dai na da alaka da rashin wani abun a zo a gani da Man U din ta kasa tabukawaa  kakar wasar bana.

Halin Da  Manchester United Ke Ciki

Makonnin da suka gabata a wasan Chelsea da Manchester United da aka tashi kunnen doki, Ronaldo ne ya farke kwallon da Marcos Alonso ya jefa a ragarsu.

Tashi daga wasan ke da wuya, sai tsohon kyaftin din Manchester United Rio Ferdinand ya wallafa a shafinsa na Twitter cikin barkwanci cewa “Har yanzu dai matsalar Manchester United din shi ne yake cin kwallayen.”

Wannan sakon na Ronaldo yana zuwa ne a daidai lokacin da wasu magoya bayan kungiyar suke ganin zuwan Ronaldo din koma-baya kawai ya haifar wa kungiyar.

Masu irin wannan tunanin suna ganin a kakar bara sun fi kokari, amma zuwansa da suke tunanin abubuwa su gyaru, sai suka tabarbare.

Sai dai duk da haka, idan aka cire kwallayen da Ronaldo ya ci a bana, Manchester United da yanzu tana tsakanin ta takwas ko na tara ce a teburi.

Man United kafin zuwan Ronaldo

A kakar bara a daidai irin wannan lokaci, Manchester United ce ta biyu a Gasar Firimiyar Ingila a lokacin da Ronaldo din bai zo ba.

A barar, Bruno Fernandes ne yake jan kungiyar, inda ya zura kwallo 27 a kakar ta bara. Idan aka hada kokarin kungiyar na bara da na bana to za a ga cewa ba ta yi kokarin da ta yi a kakar wasannin shekarar da ta gabata.

Yaya Man United za ta kasance idan babu Ronaldo?

masu sharhi a kan al’amuran kwallon kafa na ganin cewa albarkcin kwallayen da Ronaldo ya ci wa Manchester United a bana ba take ce, ba don haka ba da kungiyar za ta iya tsintar kanta a mataki na takwas zuwa 10 ko kasa da haka, duk da cewa a yanzu tana a mataki na shida a kan teburin Gasar Firimiyar 2021/2022.

A Firimiyar Ingila, ya zura kwallo 18, inda Mohammed Salah ne kawai ya fi shi zura kwallo da kwallo 22. Idan aka cire fanareti kuma, Salah zai koma kwallo 17, Ronaldo 15., inda a Gasar Zakarun Turai ya ci mata kwallo shida.

Yiwuwar barin Ronaldo Man U

Yanzu da kungiyar ta dauko sabon koci, Ten Hag daga kungiyar Ajax.

Kocin yana da tarihin horar da ‘yan wasa sosai. Sannan kungiyarsa ta Ajax tana nuna bajinta sosai.

Sai dai wasu na masa kallon kocin kananan ‘yan wasa da kananan kungiyoyi.

Bai taba horar da babbar kungiya kamar Man U ba, ga kuma manyan ‘yan wasa. Yanzu haka rahotanni suna nuna cewa a babu tabbas kan ci gaba da kasancewar Ronaldo a kungiyar ko kuma ya bayar da damar a sayar da shi.

Sai dai yanzu za a iya cewa kwallo ya koma, kuma ba a sanin maci tuwo, sai miya ta kare.

Ina makomar Benzema idan Ronaldo ya koma Real Madrid?

Wasu rahotanni da Jaridar Mirror ta wallafa na nuna cewa akwai yiwuwar Ronaldo zai koma tsohuwar kungiyarsa ta Real Madrid wadda ake jita-jitar ta soma zawarcinsa a yanzu.

Tun bayan da Ronaldo ya bar kungiyar a shekaru uku da suka gabata, kungiyar ta yi nasarar lashe gasar La Liga har sau biyu a cikin shekaru uku. Sabanin zamanin da Cristiano Ronaldo ya yi a kungiyar na kusan shekaru goma wanda shi ma lokacin sun lashe gasar sau biyu ne kacal a karkashin jagorancin sa.

Wannan ya sa wasu suke ganin a yanzu Real Madrid bat a bukatarsa musamman ma dad an was an gaban kungiyar ke kokarin gaske wato Karim Benzema wanda a yanzu shi yake jaye da ragamar kungiyar saboda a wannan shekarar kungiyar ta yi nasarar lashe gasar La Liga da kuma nasarar kaiwa zagaye na karshe a gasar Zakarun Turai wadda za su kara da kungiyar Liverpool a 28 ga watan Mayu.

Karim Benzema, dan wasan tawagar Faransa ya taka rawar gani a wasa shida da ya buga a watan da ya gabata, a fafatawar da ya fuskanci Celta da Getafe da Sevilla da Osasuna da kuma Espanyol.

A yanzu kwazon da Benzeme ke yi a kakar wasanni ta bana ya sa aka bayyana shi matsayin gwarzon La Liga na watan Afirilu.

Hakan ya sa ake ganin cewa idan har Ronaldo ya dawo kungiyar zai iya kawar da tauraruwar Benzema wato kungiyar ta sake komawa dogaro da shi.

A bana dai Karim Benzema ya jefa kwallo a raga fiye da so arba’in a wasannin da ya buga na Laliga da na Zakarun Turai na kakar bana. Kuma wannan shi ne mafi kokarin da ya taba yi na zura kwallaye da yawa a tarihin taka ledarsa.

Idan za a iya tunawa a baya lokacin da yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ya zura kwallo 451 a cikin wasanni 438 da ya bugawa mata.

Hakan ne kuma ya kai Real Madrid ga lashe kofunan Zakarun Turai har sau hudu a cikin shekara biyar da kuma kofin Laliga har sau biyu.