✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Akwai yiwuwar samun ruwan sama da wuri a daminar bana – Gwamnati

Farkon watan Maris ake sa ran samun ruwan saman farko a bana, in ji Sirika.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya ce akwai yiwuwar samun ruwan sama da wuri a bana fiye da shekarun baya a Najeriya.

A cewarsa, hasashe ya nuna za a samu ruwan saman farko a farkon makon watan Maris a jihohi kamar Bayelsa da Ribas da Akwa Ibom da sauransu.

“Ana sa ran daminar bana ta dauki kwana 84 zuwa 283, sannan 170 zuwa 230 a yankin Abuja da kewaye,” in ji Ministan.

Ya bayyana hakan ne sa’ilin da yake jawabi a wajen taron hasashen yanayi na 2023 wanda Hukumar Hasashen Yanayi ta Kasa (NiMet), ta shirya a Abuja.

Ya ce za a samu jinkirin ruwan sama a bana a jihohin da suka hada da Katsina da Zamfara da Kano da Jigawa da Yobe da Imo da sauransu.

Sirika ya ce akwai yiwuar fuskantar daukewar ruwan sama da wuri yayin daminar bana a jihohin Osun da Ondo da Edo da Delta da Imo da Bayelsa.

Sai kuma Ribas da Akwa Ibom da wasu sassa na jihohin Ogun da Legas da Yobe da Adamawa da Neja da Nasarawa da kuma Kogi.