✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Akwai yiwuwar korar karin ministocin Buhari

Ana gudanar da taron ne don bitar ayyukan ministocin bayan cin rabin wa'adinsu na biyu.

Akwai yuwuwar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauke karin Ministocinsa daga mukamansu da zarar aikin gwajin kwazonsu da ke gudana a yanzu haka ya kammala.

Shugaban, a ranar Litinin ya bayyana cewa an kirkiri taron ne na kwana biyu, domin a yi bitar kwazon kowanne minista yayin da aka ci rabin zangon wa’adi na biyu na mulkin gwamnatin.

Ministoci da Manyan Sakatarorin gwamnatin Tarayya ne dai ke halartar taron wanda ya mayar da hankali a kan muhimman bangarori guda tara da gwamnatin ta fi mayar da hankali a kansu.

Buhari dai ya ce zai zauna ya saurari dukkan abin da zai wakana yayin taron, sabanin a baya da yake halartar iya bikin budewa kawai.

Shugaban, lokacin da yake jawabi a yayin bude taron, ya yi gargadin cewa ya zama wajibi kowanne Minista da Babban Sakatarensa su dauki aikin da ke gabansu da gaske.

Ya ce taron zai kuma bayar da damar bibiyar abin da kowacce ma’aikata ta aiwatar a cikin shekaru biyun da suka gabata a kokarin gwamnatin na cika wa ’yan Najeriya alkawuran da ta dauka.

A watan Satumban da ya gabata ne dai Buhari ya kori Ministocin Aikin Gona, Sabo Nanono da na Wutar Lantarki, Saleh Mamman saboda rashin tabuka abin a-zo-a-gani.

Wannan ne dai karon farko da Shugaban ya taba korar Minista tun da ya fara mulki a 2015.

Shi kuwa da yake jawabi yayin taron, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya ce akwai kimanin kwangilolin ayyuka 878 da Majalisar Zartarwa ta bayar.

Ya ce yawancin ayyukan sun fi mayar da hankali ne wajen bunkasa rayuwa da tattalin arzikin ’yan Najeriya.