✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Akwai yiwuwar kudin kiran waya da na data ya karu a Najeriya’

Da zarar an kammala shirin, farashin kira da na data zai iya karuwa.

Hukumar Kula da Kamfanonin Sadarwa ta Kasa (NCC) ta ce tana gudanar da wasu sauye-sauye a kan kudaden gudanarwa da kamfanonin ke biya a kowacce shekara (AOL) da kuma farashin ayyukan da suke amfani da su.

NCC ta ce manufar sauye-sauyen ita ce daidaita gudunmawar da bangaren sadarwa ke bayarwa ga tattalin arzikin kasa daidai da zamani.

Aminiya ta gano cewa idan aka kammala sauye-sauyen, akwai yiwuwar farashin kudin kira da na data za su iya karuwa a Najeriya.

Shugaban hukumar ta NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta ne ya bayyana hakan ne yayin wani taron jin ra’ayin jama’a a Abuja ranar Alhamis.

Ya ce kwaskwarimar za ta kawo gasar inganta ayyuka tsakanin kamfanonin sadarwa.

“Muna sa kuma ran wadannan sauye-sauyen za su taimaka wajen sake karfafawa tare da kawo gasa mai amfani a kasuwar sadarwa ta Najeriya.”

Farfesa Danbatta ya kuma ce shirin zai taimaka wa hukumar ta kai ga gaci wajen aiwatar da babban aikinta na raba amfani da arzikin kasa na bangaren sadarwa yadda ya kamata, kamar yadda sashe na 21 na dokar da ta kafa hukumar a 2003 ya tanada.

Shugaban ya kuma ce taron jin ra’ayoyin jama’ar ba wai kawai yana nuna yunkurin NCC na inganta harkokin sadarwa kawai ba ne, ’yar manuniya ce kuma kan yadda take sauraron jama’a kafin ta dauki kowane irin matakin da ya shafe su.

“Kazalika, hukumar NCC ta kuma fara shirin girke na’urorin fasahar 5G a Najeriya, kuma nasarar yin hakan ta dogara ne kacokam kan yadda za a yi amfani da na’urorin,” inji Farsesa Danbatta.