✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwatin zabe 729 aka lalata a harin Anambra —INEC

Wannan ba zai hana gudanar da zabe ba, in ji ta

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce an lalata mata kayan aiki da daman gaske a harin da aka kai ofishinta a Anambra.

A ranar Talata ’yan bindiga suka kai wa ofishin na INEC da ke yankin Karamar Hukumar Idemili ta Kudu a jihar hari.

“Wani bangare na ginin ya lalace, haka ma duka kujeru da wasu kayayyakin da aka raba kwanan nan na shirin zaben 2023.

“Kayayyakin da muka yi asarsu a harin har da akwatin zabe 729 da teburin jefa kuri’a 243 da jakunkuna 256 da janareta” da sauransu, in ji hukumar.

Babban Kwamishinan INEC, Festus Okoye, shi ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja.

Ya ce Kwamishinar INEC ta Jihar Anambra, Dokta Queen Elizabeth Agwu, ita ce ta kai wa hedikwatar INEC rahoton abin da ya faru.

INEC ta ce duk da dai ta yi asarar kaya masu yawa sakamakon harin, sai dai sauran Katin Zaben da ke jibge ba a zo an karba ba suna nan babu abin da ya same su.

Kazalika, ta ce da alama harin shiryayyen al’amari ne musamman idan aka yi la’akari da yadda ya hada da ofishin ’yan sanda da ke yankin Nnobi a karamar hukumar.

Okoye ya bai wa al’ummar yankin tabbacin za a maye gurbin kayayyakin da suka lalace ba da jimawa ba, tare da cewa babu abin da zai hana zabe mai zuwa gudana a yankin.