✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Al-Jawda ta yaye mahaddata Alkur’ani 14 a karo na biyu

Makarantar ta yaye dalibai mahaddatan Alkur'ani a karo na biyu.

Madarasatul Al-Jawda Li Tahfizul Kur’an da ke Jihar Gombe ta yaye mahaddata Alkur’ani 14 a karo na biyu.

An kafa Madarasatul Al-Jawda ne a ranar 12 ga watan Maris na shekara ta 2012, inda suka fara karatu da dalibai 13 ta kuma fara yaye dalibai 29 a karon farko a 2018, wanda a yanzu kuma ta yaye dalibai maza hudu da mata 10 a karo na biyu.

An fara karatu a makarantar ne a zauren gidan Alhaji Yusuf Mamman Yola har ta kai matakin da daliban suka fara yawa.

A yanzu haka makarantar na da dalibai sama da 600, wanda ganin suna kara yawa ne wani tsohon dan Majalisar Wakilai, Alhaji Bello Sulaiman ya ba su kyautar gida suke karatu a ciki.

Da ya ke jawabi a wajen bikin yaye daliban, shehin malami a Jihar Gombe, Sheikh Adamu Muhammad Dokoro, ya ce samun mahadda Al’kur’ani a cikin jama’a babbar nasara ce domin Annabi (SAA) yana alfahari da hakan, saboda mahaddatan su ne jakadun Allah a doron kasa.

Sheikh Dokoro, ya yi kira ga mahaddatan da cewa kar ganin sun samu haddace Alkur’ani hakan ya sa su girman kai domin dabi’ar wasu matasa ke nan a halin yanzu, da har iyayen da suka yi musu hidima suka samu karatun suke yi wa kallon jahilai saboda ba su haddace Alkur’ani ba.

Malamin ya kuma ce rashin girmama iyaye ko malamai na debe albarka a karatun da aka yi.

Sannan sai ya yi kira ga iyaye da cewa su daure su rika biyan kudin makarantar ’ya’yansu saboda ba wasu kudi ne masu yawa ba duba da yadda ake kashe kudi a karatun boko.

Uban taro Sarkin Gona, Alhaji Umar Abdulkadir Abdulsalam, wanda ya samu wakilcin Hakimin Bogo, Umar Baddi Galadima, jan hankalin malamai ya yi da su dage wajen cusa wa yaran tarbiyya da nuna musu illar shan miyagun kwayoyi domin yanzu zamani ya lalace, yara sun koma mashaya wanda hakan yakan kai su ga aikata manyan laifuffuka.

Ya kuma taya mahaddatan murna da fatan alheri domin a cewarsa duk wanda ya haddace Alku’rani abun a yi mishi murna ne; Amma duk da haka bai gama karatu ba yanzu ne zai fara domin akwai bukatar fadada ilimin zuwa na littatafan ilimi.

Shi ma shugaban makarantar, Malam Ahmad Yusuf Khalifa, cewa ya yi duk da dai sun samu wanda ya ba su gida aka rushe aka gina makarantar, amma yanzu haka ma wajen ya yi musu kadan suna neman bayin Allah su shigo su bada gudummawarsu don ganin yadda za a sake fadada makarantar.

Daga nan ya gode wa Alhaji Bello Sulaiman, wanda ya ba su wannan gida da kuma irin gudummawa da Sanata Muhammad Danjuma Goje, ya ba su don gudanar da aikace-aikacen makarantar.