✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al-Qaeda ta wallafa littafi kan yadda ta kai wa Amurka hari a 2001

Littafin ya fita ne ranar da ake cika shekara 21 cif da kai harin

Kungiyar Al-Qaeda a ranar Lahadi ta fitar da wani littafi da ta wallafa da ke dauke da cikakkun bayanai kan yadda ta tsara kai wa kasar Amurka hari ranar 11 ga watan Satumban 2001.

Fitar da littafin na zuwa ne a daidai ranar da ake cika shekara 21 cif da kai harin wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 3,000 a wurare uku na kasar.

Daya daga cikin manyan ’yan kungiyar, Abu Muhammad al-Masri, wanda rahotanni suka ce an hallaka shi a kasar Iran a shekarar 2020 ne ya rubuta littafin.

A cikin littafin mai shafi kusan 250, kungiyar ta ce tun lokacin da ta shiga kasar Afghanistan a shekarar 1996 ta fara tsara kai harin, da nufin jefa Amurka cikin halin yaki.

Littafin ya ce wani matukin jirgin sama dan kasar Masar ne ya kawo shawarar daukar jirgin fasinja makare da makamashi tare da tukarar wani muhimmin gini a kasar ta Amurka, kamar yadda littafin da sashen intanet na kungiyar mai suna As-Sahab ya wallafa.

Daga bisani an zabi wasu mayaka da aka fara ba su horo a shekarar 1998 sannan aka tura su makarantun koyar da tukin jiragin sama a sassa daban-daban na duniya.

A watan da ya gabata ne dai sojojin Amurka suka ce sun kashe shugaban kungiyar ta Al-Qaeda, Ayman al-Zawahiri a Kabul, babban birnin Afghanistan.

Tun a shekarar 2011 Al-Zawahiri ya karbi ragamar jagorancin kungiyar daga hannun Osama Bin Laden a wata maboyarsa da ke kasar Pakistan.

Sai dai tun bayan kisan Al-Zawahirin, har yanzu kungiyar ba ta sanar da sabon shugabanta ba.

A ranar 11 ga watan Satumban 2001 ne dai Alqaedan ta kwace jirage guda hudu sannan ta rikito da su a sassa daban-daban na Amurka.

Harin dai shi ne ya jawo sojojin Amurkan suka mamaye kasar Afghanistan, kuma suka ci gaba da zama a cikinta har sai a bara da suka janye dakarunsu daga kasar bayan shekara 20. (NAN)