Alaba ya ci gajiyar lambar Sergio Ramos a Madrid | Aminiya

Alaba ya ci gajiyar lambar Sergio Ramos a Madrid

David Alaba ya ci gajiyar lambar Sergio Ramos
David Alaba ya ci gajiyar lambar Sergio Ramos
    Ishaq Isma’il Musa

A Larabar da ta gabata ce Real Madrid da gabatar da David Alaba a matsayin sabon dan wasanta da zai fara haska wa a kakar mai zuwa.

Shugaban kungiyar, Florentino Perez, ya bai dan wasan riga mai dauke da lamba hudu, wacce ita ce tsohon kyaftin din kungiyar, Sergio Ramos ya goya kafin rabuwarsa da kungiyar a bana.

Bayan an kammala gabatar da tsohon dan wasan na kungiyar Bayern Munich, sai ya gana da ’yan jarida ta yanar gizo.

Lokacin da aka gabatar da David Alaba

Lokacin da David Alaba ke ganawa da ‘yan jarida ta yanar gizo

Lokacin da David Alaba ya daga riga mai dauke da lamba hudu

Ramos ya koma Paris Saint Gernain da taka leda, bayan rashin cimma daidaito na tsawaita masa kwataraginsa da ya nemi Real Madrid ta yi a karshen watan Yunin bana.

Kazalika, Alaba yarjejeniyarsa ce ta kare a Bayern Muncich a kakar da ta gabata, lamarin da ya bashi damar komawa Real Madrid da ta taka leda kan kwantaragin kaka biyar.