✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Kudina: Al’adar biyan bashi da yara mata a Kuros Riba

’Iya yawan auren bashinka, iya mutuncinka, a al'ummar Becheve

Kabilar Bechebe da ke Jihar Kuros Riba na da wata tsohuwar al’ada wacce idan ana bin mutum bashin kudi zai aurar da ’yarsa ko yaransa kanana ga wanda ke bin kudin a matsayin biyan bashin.

Wannan rahoton ya duba rayuwar da irin wadannan kananan yara da aka aurar ta wannan hanya ke kasancewa a ciki inda suke zama tamkar abin biyan bukatar sha’awa kawai da kuma yadda har yanzu wannan al’ada ke ci gaba da gudana duk da kiraye-kirayen da ake ta yi na a haramta al’adar da ke mayar da kananan matan tamkar bayi.

Yawancin mutanen da ke Karamar Hukumar Obanliku a Jihar Kuros Riba musamman kabilar Bechebe suna gudanar da wannan al’ada da suke kira ‘Auren Kudina.’

Mutanen Bechebe da adadinsu ya haura mutum dubu 150 sun warwatsu ne a garuruwa 17 da suka hada da Katele da Amana da Ogbakoko da Belinge da Ranch da Ikwette (sabuwa da tsohuwa) da Imale da Ekor da Kalumo da Yindibe da Makambe da Apambu da Belegete da Kajinga da Mangbe da Mbunu da kuma Agusor da dukkansu ke yin wannan al’ada.

Wannan al’ada ita ce tun yarinya tana ’yar kimanin shekara biyu iyaye suke bayar da ita ga wanda ya bayar da rancen kudi gare su kuma suka kasa biya har bayan wa’adin da suka yi yarjejeniya a kai.

Iyayen kan yanke shawarar biyan bashin ta hanyar mika ’yarsu ga mutumin da ke bin su bashi ko wani da ya ci gajiyar hakan.

Idan an tashi yin wannan al’ada ba a kula da shekarun yarinyar, ko da mahaifiyarta na shayar da ita ce, wacce ita din ta iya yiwuwa ‘Matar Kudina’ ne.

A wasu lokuta idan wanda ke bin bashin ya kai shekara 60 kuma ya ga yana da sha’awar yarinyar zai rika kawo wasu ’yan kyaututtuka da suka hada da kayan abinci da sauransu wadanda duk ake lissafa su a matsayin sadaki kuma yarinyar ba ta da wani zabi a kai.

Da zarar an kai yarinya gidan mutumin ta zamo mai dogaro da kanta, ita za ta dauki nauyin ciyar da kanta kuma babu mai sa ta a makaranta sai dai mazan su yi ta kwanan aure da su kawai, yayin da matan za su yi ta fama da aikin gona da sauran ayyukan gida ga mazan.

Sabanin tsofaffin matan da aka aure su ta hanyar da aka saba, irin wadannan matan kan zamo tamkar ’yan aikin gida ne kawai.

A tattaunawa da wani tsohon Shugaban Sakandaren Obudu da ke Obanliku, Mista Nnadi Bette, ya ce bai ga alamar al’ummar sun yi watsi da wannan al’ada ba.

Bette, wanda ya shafe fiye da shekara 10 yana aiki a yankin, ya ce ba a ganin mutumin Bechebe da wata kimar da zai iya tsayawa ya yi magana a wajen taro matukar bai yi irin wannan sa-dakar ba.

“Idan kuma ya mutu ba zai samu wata gagarumar jana’izar da ta kamata ba,” in ji shi.

Ya ce, “Yawanci ‘Matar Kudina’ takan zo ne a matsayin mace ta biyu bayan ta farko ta haifi manyan ’ya’ya.

“Sukan zo a matsayin masu ilimi wanda dangin mijin ke kallo a matsayin ganimar dangi kuma na’uarar hayayyafa.”

Mista Bette ya ce da zarar sun shigo za su fara haihuwa ne tun daga shekara 15, idan ta auri mai kimanin shekara 50 ne da ake sa ran zai mutu bayan shekara 65 zai bar mata kananan yara ne daga shekara 4 zuwa 12 da ba su isa komai ba, sannan babu wani tsayayye da zai dauki nauyinsu a cikin dangin.

Binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa yawanci irin wadannan mata idan mijinsu ya rasu sukan sake aure ne a dangin tsohon mijinta wanda in ba a samu mai son ta a ciki ba, sai ta ci gaba da kwana da duk namijin da ke gidan don ci gaba da haifa musu ’ya’ya.

“Na tuna da wata daliba a da ta yi irin wannan aure ga wani matashin Bechebe mazaunin Amurka.

“Bayan na gan ta da ciki shi ne nake tambayarta cikin na wane ne, nan aka shaida min cewa ai duk namijin da ke dangin mijinta na da ikon kwanciya da ita!

“Irin wannan tsari da al’adar ba ta yi daidai da wannan zamani ba domin hakan tsantsar bautarwa ce ga ’ya’ya mata kuma ya kamata a yi watsi da ita,” in ji Mista Bette

Wani dalilin da zai sa a yi wuyar barin wannan al’ada shi ne yadda ake ganin aikata hakan a matsayin alamar cika da isa ga mutum, inda majiyoyi da dama suka shaida wa wakilinmu cewa abin da ya sa gwamnati da kungiyoyi suka kasa hana wannan al’ada shi ne kafar ungulu da wasu da ake ganin fitattu ne da suke kallon al’adar a matsayin nuna isa ga matsayin mutum.

Ya ce a al’adar mutanen wurin, iya matsayinka a cikin al’umma shi ne iya yawan irin wadannan matan da mutum ya tara.

Wata majiyar ta ce, “A al’adar Bechebe ba a ganin mutum a matsayin cikakken magidanci matukar ba shi da irin wadannan mata.”

Rayuwar ‘Matar Kudina’ ke kasancewa

A tattaunawar Aminiya da matan da suka tsinci kansu a irin wannan yanayi, wata mai suna Dorathy Etagwa Philips, ta ce tun tana ’yar shekara biyar aka bayar da ita a irin wannan auren.

“Yanzu shekaruna 27 kuma mijina mai kimanin shekara 77 yana nan da rai.

“Ni daya ce daga cikin matansa na sa-daka.

“Ba na jin dadi kwata-kwata da irin wannan auren karfi da yaji, amma babu yadda zan yi yanzu don na haifi ’ya’ya biyar tare da shi.

‘Bauta da ukuba kawai na sani’

“Ban taso na san abin da ake kira soyayya ba, abin da na riska kawai shi ne ukuba da bauta,” inji ta.

Ta kara da cewa sa’o’inta mata yanzu sun kammala jami’a kuma suna abin kansu, sabanin ita da aka mayar da ita masana’antar haihuwa da rainon yara kawai.

Ta ce, “Na sha wahala matuka wajen ciyar da maigidana da ’ya’yan da na haifa masa.

“Al’adar ita ce dole in yi aiki don nemo musu abin da za su ci.

“Nakan sha wahala a aikin gona tun daga safiya zuwa maraice, kuma a karshe ba ni da damar sarrafa abin da na noma don amfanin kaina, domin da ni da abin da na mallaka duka kayan maigida ne.

“Dole in yi duk abin da yake so kuma idan na gudu na bar gidan to a haka ’ya’yana za su kasance su ma.

“Za su sayar da su musamman mata daga cikinsu amma matukar ina gidan, to ina da ikon in ce ban yarda a bayar da ’ya’yana ga irin wannan aure ba.

“Ba na son ’ya’yana su fuskanci irin abin da na fuskanta.

“Idan na gudu za su yi amfani da wani nau’in tsafi da ake kira ‘Olambe’ don kamo ni da kuma hallaka ni tare da ’ya’yana.

Wannan ne abin da ya tilasta min zaman gidan amma babban abin takaici ne yadda ake sayar da mace tun daga ’yar shekara daya a duniya da sunan aure.”

Tsoron tsafin Olambe

Mutanen sun yi amanna cewa ta hanyar wannan tsafin akan gano tare da azabtar da macen da ta yi kokarin gudu tare da sa mata ciwo da nau’o’in azabtarwa da kuma kisa.

Wani dan yankin da ke zaune a garin Kalaba mai suna Wilberforce Etun ya ce “yadda wannan camfi ke amfani shi ne ta hanyar shafa wa matar maganin da duk inda ta je da kanta za ta dawo.

“Akan yi amfani da tsafin ne ta hanyar ambaton sunan matar sau bakwai daga nan sai a daure Dodon Olambe tamau ta yadda in ta ki dawowa tsafin zai hallaka ta.

“Zai iya sa maganin a duk wani rami ko wata kafa da ke jikin iccen gwanda wanda da zarar ya yanke itaciyar, to a nan take matar za ta mutu a duk inda take.

“Sannan idan ya kara maganin a bakin wuta to matar za ta shiga tsananin ukuba da jin zafi a jiki kafin ta mutu, yayin da idan ya jefa a cikin ruwa kuma za ta kumbura kafin ta mutu,” in ji Utuame Linus.

Yadda yunkurin dakatar da al’adar ke haifar da gaba mai tsanani.

Mutanen Becheve ba sa jin dadin ganin yadda kafafen yada labarai ke ruruta wannan batun don janyo hankalin masu ruwa-da-tsaki a kai, duk da cewa duk da wannan kalubalen ana samun masu ruwa-da-tsakin da ke mara wa gwamnati da kungiyoyi baya don ganin an kawar da wannan mummunar al’ada.

Wani fasto kuma mai rajin kare hakkin jama’a a Jihar Delta da ya kwashe shekara 27 yana kamfen din kin jini da nuna kyama ga wannan mummunar al’adar, da ya roki a boye sunansa da na cocinsa saboda kiyayyar da yake fuskanta kan batun ya ce, “Har yanzu muna ci gaba da fafatawa a kan wannan batu amma ta gefen Kamaru. Mun yi tarurruka da dama.

“Har yanzu ba zan iya kai ka zuwa Becheve da kaina ba saboda kiyayayyar da ake nuna min a can.

“Daya daga cikin cocinmu da ke Keyi har yanzu yana kulle saboda mun ceci wata yarinya mun boye ta a ciki.”

Da yake tofa albarkacin bakinsa game da wannan al’ada, Gwamnan Jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade, ya ce duk lokacin da wata al’ada ta yi hannun riga da dabi’a ta hankali da wayewa ko kuma take cin karo da dokokin shari’a na kasa, to, dole ne a dakatar da ita.

“Dokokinmu sun bayyana cewa ’yan Najeriya, ciki har da kananan yara suna da ’yanci da mutuncin da duk wanda ya yi kokarin keta su ya zama mai laifi.

“Sai dai yana da matukar wuyar sha’ani a duk lokacin da kake tunkarar fada da irin wannnan matsla ta al’ada da kuma dokokin kasa da suke karbabbu.

“Ba za mu yi ta kama jama’a muna garkame su a gidan kaso a matsayinmu na gwamnati ba, mutane suna bukatar a ilimantar da su a wayar musu da kai a kan munanan abubuwan da suke aikatawa, wannan shi ne abin da muka fi mayar da hankali a kai,” in ji shi.

Kungiyoyi na fafutikar haramta al’adar ‘Matar Kudina’

Kungiyar kare hakkin mata mai suna TINAF, wacce wata lauya mai suna Misis Imah Nsa Adegoke ke shugabanta, tana matsa wa gwamnatocin jihohi lamba su yi koyi da Jihar Kuros Riba wajen kafa doka Mai lamba 10 ta shekarar 2007 mai taken ‘Dokar Kayan Gadon Mace’ don ceto mata daga kangin bautar da ake jefa su da kuma watsi da ake yi da lamuransu.

Kungiyar ta yi kira ga sarakuna 18 da ke jihar su sa baki don kawo dauki wajen

ganin an farfado da dokar a jihar.

“Wannan dokar za ta ceto mata musamman zawarawa domin za ta ba su kariya.

“Hatta yaran da ake haifar su a wajen aure matukar iyayensu maza sun amince da su a matsayin ’ya’yansu wannan dokar za ta ba su kariya daga mugayen kishiyoyi.

“Muna so a aiwatar da wannan dokar,” inji Adegoke.

Ita ma Shugabar Tsare-Tsare na Kungiyar Girls Power Initiative (GPI), Misis Ndodeye Bassey, ta ce Najeriya ta sa hannu a kudirori da dama na duniya da ke magana kan batun kare hakkin mata da kananan yara da hana cin zarafinsu.

Ta yi kira ga ’yan sanda su kara horar da jami’ansu da sauran jami’an tabbatar da tsaro ta yadda za su san yadda sababbin dokokin kariya ga mata da yara suke.

A watan jiya ne Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwa da Cibiyar Shugabanci, Tsare-Tsare da Ci-Gaban Afirka (ACLSD) suka shirya tarurruka a garuruwan Sankwala da Becheve kan yaki da cin zarafin mata da nufin kawar da al’adar.

Babban Daraktan ACLSD, Monday Osasah, ya ce taron wayar da kan zai taimaka wajen kawar da tsohuwar al’adar da ke cin zarafin ’ya’ya mata ciki har da auren ‘Matar Kudina.’

A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Obanliku, Rabaran Akasin Joseph ya ce yakan ziyarci coci-coci a wasu lokuta don gabatar da jawabi kan bukatar sake duba wannan al’ada wadda kuma sukan isar da sakon ga mabobinsu.

Sarkin Obanliku, Mista Uchua Amos ya ce sun fara shirin ruguza wannan al’ada tun daga tushe ne kuma sun yi nasarar farawa daga mai wuya zuwa mai sauki inda suka sa bangaren Majalisar Dokoki kirkirar dokokin da za su haramta al’adar kwata-kwata.

Ya ce ya dade da burin kawar da wannan tsohuwar al’ada tun bayan darewarsa karagar sarauta shekara biyar da suka wuce.

Ya ce masarautarsa na iya nata kokarin amma abin na bukatar lokaci kasancewar al’adar dadaddiya ce a dogon zamani.

“Ba cikin kankanin lokaci ne za a iya kawar da wannan al’ada ba ana bukatar isasshen lokaci wajen wayar da kan jama’a tare da samun goyon bayan gwamnati.

“Ba ma bukatar irin wannan al’ada a wannan karni da zamani da ake ciki.

“Hakan ya saba wa ’yan Adamtaka,” in ji Sarkin.

Shugaban kabilar Bechebe, Mista Sunday Ichile cike yake da burin ganin bayan hakan inda ya ba Sarkin cikakken goyon bayansa kan yunkurin kawar da al’adar.