✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alarammomin Kano sun gudanar da addu’o’i na musamman don samun tsaro da shugaba na gari

Akalla alarammomi da sauran al'ummar Musulmi mutum 3,000 ne suka halarta taron addu'o'in na Musamman

Akalla alarammo da sauran al’ummar Musulmi 3,000 ne a Jihar Kano suka gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya a Najeriya, da kuma a lokacin zaben 2023.

Shugaban Kungiyar Makaranta Alkur’ani ta Najeriya (KURAN), Gwani Lawi Gwani Danzarga, ya ce an gudanar da wadannan addu’o’i ne domin samun zaman lafiya a fadin Najeriya da kuma ganin an gudanar da sahihin zabe cikin gaskiya da adalci a 2023, lura da yadda gabatowar zaben ke sanya fargaba a zukatan jama’a.

“Kowa ya san halin da ake ciki na rashin tsaro a kasar nan, ga shi kuma zaben 2023 yana kara karatowa, saboda haka akwai bukatar mu yi addu’o’i na musamman domin wanzuwar zaman lafiya a Kasar nan,” inji Gwani Lawi.

Ya ce, “A matsayinmu na Musulmi, mun yi imani cewa babu wata matsala ko damuwa da Allah ba zai iya magancewa ba.

“Shi ya sa muka kira al’ummar Musulmi su zo su mika wa Allah kokensu domin Ya zaba mana shugaba nagari da zai sauke nauyin shugabancinmu da ya rataya a wuyansa.

“Allah Ya san halin da muke ciki, mun sallama maSa al’amarinmu, Ya zaba mana shugaban da zai yi wa kasar nan jagoranci na gari ya kawo mata cigaba da daukaka ba tare da la’akari da inda ya fito ba.

“Mun kuma roki Allah Ya sa a yi wannan zabe da ke kara karatowa lafiya, cikin kwanciyar hankali.”

Addu’ar da aka gudanar a Masallacin Gwani Danzarga da ke unguwar Kogi a birnin, Kungiyar Alarammomi ta Najeriya (KURAN) ce ta shirya shi tare da Kungiyar Mata ta Matasa Masu Wayar da Kai Game da Siyasa (YOWPA) da kuma Hadaddiyar Kungiyar ’Yan Kasuwa ta Najeriya (AMATA).

A nata jawabin, Shugabar Kungiyar YOWPA, Hajiya Asmau Sarki Mukhtar, ta ce sun yi hadin gwiwa da alarammomi da sauran kungiyoyin ne domin wayar da kan matasa da matan Jihar Kano kan muhimmancin shiga harkokin siyasa.

Ta ce, “Mun wayar da kan matasa domin kada su bari a yi amfani da su wajen bangar siyasa ko kawo hargitsi a lokacin zabe.”

Ta kuma yi kira ga ’yan siyasa da su ji tsohon Allah, sannan duk abin da za su yi a lokacin zaben, ya kasnace sun yi shi ba tare da kawo tashin hankali ba.