✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’an gwamnati da albashinsu ya ninka na Buhari

Hukumar RMAFC ta ce akwai jami'an gwamnati da kudin sallamarsu ya ninka na shugaban kasa sau hamsin

Hukumar Tsara Albashi ta Kasa (RMAFC) ta bayyana cewa akwai jami’an gwamnati da albashinsu ya ninka na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sau hudu.

Shugaban hukumar, Mohammed Shehu, ya bayyana cewa akwai ma’aikatan gwamnati da kudin sallamarsu ya ninka na shugaban kasa sau hamsin, inda suke karbar Naira miliyan 500, shugaban kasa kuma ke karbar miliyan N10.

Ya ce, “Albashin shugaban kasa a wata bai kai Naira miliyan daya da dubu 300 ba.

“Yanzu akwai ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu da albashinsu ya ninka wannan (albashi) har sau hudu,” in ji shi, a tattatunawarsa da shirin ‘Sunrise Daily’ na tashar talabijin ta Channels.

Shugaban na RMAFC, ya ce, “A shekarar 2008 N1.3m kudade ne masu kauri, amma yanzu akwai ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu da albashinsu ya ninka wannan har sau hudu.”

Ya jaddada cewa albashin shugaban kasa bai kai na wasu ma’aikatan hukumomin gwamanti irinsu Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA) da Babban Bankin Najeriya (CBN) da Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), da Hukumar Kula da Teku (NIMASA) ba.

A cewarsa, NPA na daga cikin hukumomin da suka fi tara wa gwamnati kudaden shiga, inda a wata shida na farkon 2022 ta tara biliyan N172.

A cewarsa, akwai nau’ika 17 na albashin ma’aikatan gwamnati a Najeriya, don haka ya bukaci a tsara albashin jami’an gwamnati ta yadda babu wanda nasa zai fi rabin na shugaban kasa.

“Ina nufin kada albashin wani jami’in gwamnati ya fi na shugaban kasa, amma yanzu akwai ma’aikatan gwamnati a NCC, NIMASA, NPA da CBN da albashinsu ya fi na shugaban kasa,” in ji shi.

Ya ce nan gaban hukumar za ta aiwatar da karin albashin alkalai da na sauran jami’an gwamnati daidai da yadda rayuwa ta yi tsada.

Da aka tambaye shi game da ko gwamnati za ta iya kara wa ma’aikata albashi a wanna halin da ake ci, sai ya soki yadda wasu hukumomin gwamnati ke kashe kudaden da suke tarawa.

A cewarsa, a halin yanzu akwai kudaden shiga da yawansu ya kai kusan Naira tiliyan bakwai da wasu hukumomi suka ki sanyawa a asusun Gwamnatin Tarayya.

Don haka ya yi kira ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta binciki hukumomin da hakan ta shafa.

Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da hanzarta aiwatar da rahoton Kwamitin Steve Oronsaye da ya ba da shawarar hadewa ko rusa wasu hukumomi domin rage yawan kudaden da gwamanti ke kashewa kan gudanarwa.