✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aleiro ya kayar da Gwamnan Kebbi a kujerar Sanata

Zaben na daya daga cikin mafiya zafi a Najeriya

Tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Adamu Aleiro, na jam’iyyar PDP, ya kayar da Gwamnan Jihar mai ci, Atiku Bagudu na APC a kujerar Sanatan Kebbi ta Tsakiya.

Jami’in Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) mai kula da sakamakon zaben, Farfesa Abass Yusuf Sa’id ne ya bayyana hakan da safiyar Talata.

Ya ce Aleiro ya sami kuri’a 126,588 inda shi kuma Bagudu ya samu kuri’a 92,389.

An gudanar da zaben ne a Kananan Hukumomi takwas na Gwandu, Bunza, Aliero, Maiyama, Koko-Besse, Jega, Kalgo da kuma Birnin Kebbi.

Dana ana ganin zaben a daya daga cikin wanda ya fi zafi a Najeriya.