✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda alhazai suke tsayuwar Arafa

Alhazai za su shafe yinin yau suna ibada da addu'o'i a Filin Arafa.

Alhazai 60,000 da ke halartar aikin Hajjin bana sun isa filin Arafa inda za su shafe yinin Litinin suna gudanar da ibada da addu’o’i da kuma neman gafara.

Alhazai sanye da takunkumi da ke aikin Hajjin sun baro sansaninsu da ke Mina suka kwana ne a Filin Arfa, inda za su halarci babbar ibadar da a baya miliyon mahajjata ke halarta daga ko’ina a fadin duniya.

Sai sabanin shekarun baya da ake ganin mahajjata babu masaka tsinke a kan Dutsen Rahama, wanda aka fi sani da Dutsen Arafa, bana ma abin ya bambanta.

Halartar tsayuwar Arfa 9 ga Dhul-Hijja, 1441 Hijiriyya shi ne kololuwar aikin Hajji, kuma daya daga ciki shika-shikan Musulunci.

Alhazan, wadanda daukacinsu mazauna kasar Saudiyya ne, za su yi sallolin Azahar da La’asar a Arfa, inda a bana Limamin Masallacin Harami, Sheikh Bandar Baleelah, zai gabatar da huduba.

A filin Arfa ne aka ruwaito cewa Manzon Allah (SAW) ya gabatar da hudubarsa ta karshe sama da shekara 1,400 da suka gabata.

Gabanin faduwar rana alhazan za su tafi Muzdalifah — tsakanin Arafat da Mina — su kwana, kafin washegari su koma Mina su yi “jifar shaidan”.

– ’Yan gata –

Selma Mohamed Hegazi, ’yar kasar Masar ta ce kasancewa daga cikin masu rabo “zai sa ka ji cewa lallai Allah mai gafara ne kuma Ya zabe mu mu halarci a wannan wurin. In Allah Ya yarda addu’o’inmu za su karbu” .

Ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “Duk jikina ya sai rawa yake ta yi,” a lokacin da take tsaye a tsakanin sauran mahajjata sanye da harami.

A yayin da masu ibadar suka halarci Filin Arafa a cikin yanayi na natsuwa, Baref Siraj, dan kasar Saudiyya mai shekara 58 ya ce, “Hakika kasancewata cikin mutum 60,000 da ke aikin Hajji …. babbar ni’ima ce.”

Aikin Hajji daya ne daga cikin manyan tarukan addini a duniya, wanda sama da mutum miliyan 2.5 ke halarta a lokaci guda kuma a wuri guda.

Gudanar da aikin Hajji lamari ne mai matukar daraja ga mahukuntan Saudiyya, wadanda su ne Hadiman Masallatai biyu Masu Alfarma.

Hana mahajjata daga wajen kasar ya haifar da matukar damuwa tsakanin Musulmin duniya, wadanda yawanci suke yin ajiya ta  shekaru domin su samu halartar ibadar.

An zabi mahalarta daga cikin mutum 558,000 da suka nemi damar ta hanyar tsarin tantancewa ta intanet.

An kuma takaita halartar idabar ga mutane masu shekara 18 zuwa 65 da suka kammala daukar allurar rigakafin cutar COVID-19 kuma ba sa fama da wata cuta mai tsanani.

– Zama lafiya… –

Mahukuntan Saudiyya na fatan a bana za a samu karin nasara a kan wanda suka samu wajen gudanar da aikin a bara.

Wannan shi ne aikin Hajji na biyu wajen karancin alhazai, bayan na 2020 wanda mahajjata 10,000 suka halarta sakamakon bullar cutar COVID-19.

A ranar Lahadi, Hukumar Lafiya ta Saudiyya ta ce baba ko mutum daya a cikin alhazan da ya kamu da cutar ba.

Yanzu mutum sama da 509,000 ne suka kamu da cutar a kasar inda ta yi ajalin mutum sama da 8,000.

Kawo yanzu an yi wa mutum akalla miliyan 20 allurar cutar a kasar mai yawan al’ummar sama da miliyan 34.

– Sabon salo –

Kasancewar aikin Hajji ya saba tara mutane masu yawan gaske, wanda ke iya sanadin yaduwar cutar, gwamnatin Saudiyya ta ce da dauki “tsauraran matakan kare lafiya” domin hana yaduwar sabon samfurin cutar.

Daga cikin matakan, an kasa alhazan zuwa rukuni 20 domin hana yaduwar cutar.

An kuma samar da katunan zamani da alhazai suke yin amfani da su domin samun masauki da ababen hawa ba tare da haduwa da jami’ai ba.

Akwai kuma butum-butumi da aka kera domin raba wa mahajjata ruwan Zamzam a Masallacin Harami.

Ibrahim Siam mai shekara 64 dan kasar Masar ya ce fasahar zamanin da aka yi amfani da su sun taimaka matuka wajen saukaka aikin Hajjin bana.