✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ali Jita: Kannywood ta girgiza da rasuwar mahaifinsa

Akalla mutum 300 daga Kannywood sun bayyana kaduwa da rasuwar mahafin Isah Ali Jita

Masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood ta cika da alhinin rasuwar mahaifin shararren mawakinta, Isah Ali Jita.

Akalla mutum 300 ne daga Kannywood suka yi wa Ali Jita ta’azziyya ta shafukansu na sada zumunta bayan samun sanarwar rasuwar da mawakin ya fitar.

“Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un, cikin alhini ina sanar da rasuwar mahaifina, Alhaji Isah Jibril Kibiya, ….Allah Ya sa ka huta, Ya yafe maka kura-kurenka Ya sa Aljanna ta zame maka makoma,” kamar yadda mawakin ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Asabar.

Hoton da Ali Jita ya wallafa a shafinsa na Instagram

Bayan wallafa rasuwar mahaifin nasa, masu ba da umarni, shiryawa da jarumai da suka yi wa Ali Jita ta’aziyyar su hada da Ali Nuhu, Abdul Amart Maikwashewa, Abdul M. Shariff, Rahama Sadau, Zainab Abdullah da Fresh Emir.

Sauran ’yan sahun farkon masu ta’aziyyar sun hada da Rukayya Dawayya, Nazifi Asnanic, Nuhu Abdullahi, Ayshatul Humaira, Sheik Isah Alolo, Sani Mu’azu, da Ali Gumak.

Ita ma Hannatu Umar, Salisu S. Fulani, Yakubu Mohammed, Samira M. Ahmed, Umma Shehu, Fati Muhd, Saratu Gidado da sauran daruruwan masoya na daga cikin wanda suka jajanta.

Mako biyu da suka gabata, Ibrahim Maishunku shi ma ya rasa mahaifinsa, Alhaji Labaran Maishunku bayan fama da rashin lafiya, kuma ya rasu yana da shekaru 80 a duniya.

Ali Isah Jita shararren mawaki ne a masana’antar Kannywood da aka dade ana damawa da shi a masana’antar.

Wakokinsa sun fi karkata ne zuwa ga bangaren suka shafi gidan biki ko mata.