✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aljeriya za ta ba wa Palasdinawa tallafin Dala 100m

Gwamnatin Aljeriya ta yi alkawarin tallafin Dala miliyan 100 ga al’ummar Palasdinawa da ke cikin bukata

Gwamnatin kasar Aljeriya ta yi alkawarin tallafin Dala miliyan 100 ga al’ummar Palasdinawa da ke cikin bukata.

Shugaban Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, ya sanar da hakan ne a lokacin da ya karbar bakuncin Shugaban Palasdinawa, Mahmud Abbas, a ranar Litinin.

Ya ce tallafin “Wani yanki ne na dadadden tarihin kasarsa na taimaka wa ci gaba al’ummar Palasdinawa a duk halin da suke ciki.”

Shugaban Palasdinawan na ziyarar kasashen Larabawa a yankin Kudancin Afirka ne mako biyu bayan kasar Moroko – makwabciyar Aljeirya – ta  rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da Ministan Tsaron Isra’ila, Benny Gantz.

Hakan na zuwa ne a yayin da Moroko ke shirin karbar bakuncin Babban Taron Kungyiyar Kasashen Larabawa a watan Maris na 2022, wanda shi ne taron kungiyar na farko bayan Amurka ta sa baki kasashen Larabawa sun ci gaba da hulda da Isra’ila.

Shugaban Aljeriya ya ce kasarsa “za ta yi duk mai yiwuwa don ganin taron ya mayar da hankali kacokam a kan kasar Palasdinu da kuma halin da Paladinawa ke ciki.”

Gidan talabijin na kasar Aljeriya ya ce shugaban yana kuma shirin gayyato bangarorin Palasdinawa zwau kasarsa domin tattaunawa.

Yarjejeriyar tsaro da Isra’ila ta kulla da Moroko ya haifar da damuwa a makwabciyarta, Aljeriya, wadda ke ganin hakan a matsayin barazanar tsaro a gare ta.

Wani babban jami’in tsaron Aljeriya ya yi zargin cewa Gantz ya ziyarci Morokok ne da nufin kai wa kasar Aljeriya hari.

A watan Agusta ne aka fara zaman doya da manja tsakanin Aljeriya da Moroko bayan Ajeriya ta zargi makwabciyar tata da nuna mata tsana.

Tuni dai Moroko ta musanta zargin.