✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ka yi mana magani!

Ko shakka babu a cikin kwana goma na farkon shekarar 2020 Miladiya, ayyukan ta’addanci da dama aka taho da su daga bara, sun yi matukar…

Ko shakka babu a cikin kwana goma na farkon shekarar 2020 Miladiya, ayyukan ta’addanci da dama aka taho da su daga bara, sun yi matukar kara kazancewa. An samu karuwar hare-haren ’yan bindiga da na masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa a gidaje da kan manyan titunan kasar nan. Ga kuma hare-haren kungiyar Boko Haram da a bana aka shiga shekara ta 11, ana fama da su a jihohin Arewa maso Gabas da kuma yawan kashe-kashe, walau a tsakanin dan uwa da dan uwa ko aboki da aboki ko ma daga jami’an tsaro, duk a kan abin da bai taka kara ya karya ba, sai ka ji an ce rai ya salwanta.

Wace irin rayuwa muke ciki ne? Abin sai dai mu ce ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!

Dukkan wadannan matsaloli suna faruwa ne, duk da muna ji wani lokaci ma muna ganin irin hobbasar da jami’an tsaron kasar nan suke yi da niyyar kawo karshen wannan annoba ta rashin tsaro. Rashin tsaro na cikin abubuwa uku da Shugaba Buhari ya yi alkawarin yaki da su tun a shekarar 2015 lokacin da yake gangamin neman kuri’a. Sauran biyun su ne, yaki da cin hanci da rashawa da kuma farfado da tattalin arzikin kasa.

Abin da ya sanya na kawo wannan takaitaccen bayani, bai wuce irin labarin da yayar wannan jarida ta karshen mako wato Daily Trust On Saturday ta ranar 11 ga Janairu ta buga bayan da ta yi zuzzurfan bincike kan  annobar kashe-kashen rayuka da jikkata al’umma da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da rikicin ’yan kungiyar Boko Haram da ’yan bindiga da na masu tada kayar baya da suka auku a cikin kwana 10 na farkon bana da suka yi sanadiyyar hallaka mutum 147, wasu kuma 124, aka sace su don neman kudin fansa ko don ta’addanci kawai, ko ma aka jikkata su.

Wancan adadi kamar yadda jaridar ta wallafa, kimanin mutum 39, ’yan kungiyar Boko Haram suka kashe a jihohin Borno da Yobe, tare da yin garkuwa da mutum 8, baya ga dukiyar miliyoyin Naira da suka salwanta a cikin hare-haren.

Ta fannin hadurran mota kuwa mutum 30 suka mutu, yayin da wadansu 57 suka jikkata.

Daga hare-haren ’yan bindiga kuwa, jaridar ta Daily Trust On Saturday ta kalato cewa mutum 57 aka kashe, yayin da 21 kuma aka sace su da niyyar neman kudin fansa. Ta bangaren ’yan ta’adda masu sace-sacen shanu, bin diddigin jaridar ya gano cewa mutum 6 aka kashe yayin da aka yi garkuwa da mutum 34,

Ta fannin tashe-tashen gobara, a wadancan kwana 10, mutum 15 suka kwanta dama, 3 kuma suka jikkata, ciki kuwa har da gobarar iskar gas din girki a Sabon Tasha a Kaduna wadda ta faru a ranar 4 ga Janairun inda mutum 8 suka rasu, ciki har da Shugaban Hukumar Kula da Makamashi ta Kasa Farfesa Simon Mallam da ya je aski a yankin.

Batun hare-haren Boko Haram kuwa ba a magana, kasancewar kusan a kullum sai ka ji inda aka yi artabu su da sojoji, ko ka ji sun tare hanya sun yi garkuwa da matafiya, kamar yadda suka yi a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar 9 ga wannan watan inda suka kama fasinjoji 7.

A wani hari da suka kai a Michika a Jihar Adamawa, bayan wadanda suka kashe, zuwa yanzu ana cigiyar wani Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) na yankin.

A kusan duk jihohin shiyoyin Arewa maso Yamma, irin su Katsina da Kaduna da Sakkwato da Zamfara a kullum da wuya garin Allah Ya waye, rana ta koma ga Ubangijinta, ba tare da jin labarin ’yan bindiga sun kai hari a wani kauye ko kauyuka ba, kuma sun yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa. Haka wannan mummunan labari yake a jihohi irin su Neja da Filato da Abuja Babban Birnin Tarayya da Kwara, kai har ma jihohin Binuwai da Nasarawa, dukkansu a shiyyar Arewa ta Tsakiya. Ko dai ka ji fadan Fulani makiyaya da manoma ko kuma ka ji hare-haren masu yin garkuwa da mutane ko masu satar dabbobi. Kasa dai babu kwanciyar hankali!

Duk da a jihohin Arewacin kasar nan aka fi fama da annobar rashin zaman lafiya shekara-da-shekaru, fiye da sauran sassan kasar nan, amma har yanzu gwamnonin jihohin sun kasa hada kai, balle su hada karfi da karfe ko da a zaman makwabta da makwabta, alal misali tsakanin Katsina da Zamfara ko tsakanin Yobe da Borno, su samar da wata rundunar tsaro ta hadin gwiwa da za su yaki annobar rashin tsaron da ta addabe su, sai dai kowane Gwamna ya yi gaban kansa, gaban kan da ya kasa samar da mafita.

Sai ga shi kwatsam! A ranar 9 ga wannan wata gwamnonin jihohi 6 na Shiyyar Kudu maso Yamma (Oyo, Ekiti, Ondo, Legas, Osun da Ogun) sun kaddamar da wata  gagarumar rundunar tsaro a birnin Ibadan babban birnin Jihar Oyo, mai suna Amotekun, bisa ga sahalewar Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Alhaji Muhammadu Adamu da za ta rika sintiri a lungu da sakon shiyyar baki daya. Ka dai iya cewa tamkar ’yan kato da gora da muke da su a unguwanninmu a wasu garuruwa da biranen jihohin Arewa, sai dai shirin tsaro na Amotekun ka iya kiransa tamkar ‘Murucin kan dutse,’ wanda bai fito ba sai da ya shirya, kasancewar dukkan gwamnonin shiyyar 6, da amincewarsa aka kafa shirin kuma ba wanda bai ba da motoci ashirin-ashirin ba, baya ga baburan hawa da kudaden tafiyar da shirin na yau da kullum.

Da ma tun farkon wannan jamhuriyyar gwamnonin shiyyar Kudu maso Kudu da sauran masu fada-a-ji na shiyyar suke ta matsin lamba sai Gwamnatin Tarayya ta bar su wajen kafa ’yan sandan jihohi. Shirin da gwamnonin jihohin Arewa da wasu masu fada-a-ji na Arewar suka rika sukar lamarin.

To yanzu ga gwamnonin Kudu maso Yamma da shiyyarsu, ba ta cikin mummunar barazanar tsaro irin ta jihohin arewa, sun hada karfi da karfe sun kafa rundunar tsaro ta Amotekun, rundunar da nan gaba ita za ta zama ’yan sandan jihohi, gwamnonin Arewa na kallo. Sai dai rahotanni sun nuna tuni Gwamnatin Tarayya ta bakin Atoni-Janar kuma Ministan Shari’a Alhaji Abubakar Malami ta ki amincewa da kafa rundunar tsaro ta Amotekun ya zuwa ranar Talatar da ta gabata.  Abin da yanzu muke jira mu ji kuma mu gani shi ne yadda za ta kaya a tsakanin gwamnonin Shiyyar Kudu maso Yamma da Gwamnatin Tarayya game da dambarwar kafa rundunar tsaro ta Amotekun.