Allah Madawwami | Aminiya

Allah Madawwami

    Fasto Enoch Atiyaye

Barkanmu da saduwa cikin wannan mako, a yau za mu ga bayyanuwar girman Allah Madawwami, Madaukaki da kuma rayuwarmu na ’yan Adam cikin Littafin Zabura. Bari Ubangiji Allah Ya ba mu ganewa, amin.

Ya Ubangiji! A koyaushe Kai ne wurin zamanmu. Kafin a kafa tuddai, Kafin kuma Ka sa duniya ta kasance, Kai Allah ne, Madawwami. Ba Ka da farko, ba Ka da karshe. Kakan sa mutane su koma yadda suke, Su zama kura.

A gare Ka shekara dubu, kamar kwana daya ne, kamar jiya ce wadda ta shige, gajeruwa ce kamar sa’a guda ta dare. Kakan kwashe mutane kamar yadda ambaliyar ruwa take yi, kamar mafarki suke, ba su dadewa. Kamar tsire-tsire suke wadanda suke tsirowa da safe, su yi girma har su yi huda, sa’an nan su yi yaushi su bushe da yamma.

Mun hallaka ta wurin fushinKa, mun razana saboda hasalarKa. Ka jera zunubanmu a gabanKa, zunubanmu na boye kuwa, Ka sa su a inda za Ka gan su. Fushinka Ya gajarta tsawon ranmu, ranmu ya kare kamar ajiyar zuciya. Tsawon kwanakin ranmu duka akalla shekara ce saba’in, in kuwa muna da karfi, shekara tamanin ne. Duk da haka iyakar abin da wadannan shekaru suke kawo mana, damuwa ne da wahala, nan da nan sukan wuce, tamu ta kare.

Wa ya san iyakar ikon fushinKa? Wa ya san irin tsoron da hasalarKa za ta kawo?

Ka koya mana mu sani ranmu na dan lokaci ne, domin mu zama masu hikima. Ya Ubangiji! Sai yaushe za Ka ji tausayinmu? Ka ji tausayin bayinKa! Ka cika mu da madawwamiyar kaunarKa a kowace safiya, don mu rera wakokin murna dukkan kwanakin ranmu. Yanzu sai Ka sa mu yi farin ciki mai yawa, kamar yadda Ka sa muka yi bakin ciki a dukkan shekarun nan da muka sha wahala. Ka yarda mana, mu bayinKa, mu ga ayyukanKa masu girma, Ka yardar wa zuriyarmu su ga ikonKa mai girma.

Ka yarda, albarkarKa ta kasance tare da mu, ya Ubangiji Allahnmu! Ka sa mu yi nasara game da dukan abin da za mu yi! Eh, Ka ba mu nasara a duk abin da muke yi!

Duk wanda ya je wurin Madaukaki zai zauna lafiya, duk wanda yake zaune a inuwar Mai iko duka, ya iya ce wa Ubangiji, “Kai ne kariyata da Mai kiyaye ni! Kai ne Allahna, a gare Ka nake dogara!” Hakika zai kiyaye ka daga dukkan hadarurruka da ka boye, daga kuma dukkan mugayen cututtuka. Zai rufe ka da fika-fikanSa, za ka zauna lafiya a karkashinsu. AmincinSa zai tsare ka, ya kiyaye ka. Ba za ka ji tsoron hadarurruka da dare ba, ko faɗawar da za a yi maka da rana, Ko annobar da take aukowa da dare, ko mugayen da suke kisa da tsakar rana. Mutum dubu za su faɗi daura da kai, dubu goma kuma za su fadi dama da kai, amma kai, ba za a cuce ka ba. Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta wa mugaye.Domin ka dauka Ubangiji Yake kiyaye ka, Madaukaki ne Yake tsaronka, to, ba bala’in da zai same ka, ba za a yi wa gidanka aikin karfi da yaji ba. Allah zai sa mala’ikunSa su lura da kai, za su kiyaye ka duk inda za ka tafi. Za su dauke ka a hannuwansu, don kada ka buga kafarka a dutse. Za ka tattake zakuna da macizai, za ka tattake zakuna masu zafin rai da macizai masu dafi. Allah Ya ce, “Zan ceci wadanda suke kaunaTa, zan kiyaye wadanda suka san Ni. Sa’ad da suka yi kira gare Ni, zan amsa musu, zan kasance tare da su sa’ar da suke shan wahala, zan cece su in girmama su. Zan ba su tsawon rai da lada, hakika kuwa zan cece su.”

Abu mai kyau ne a yi wa Ubangiji godiya, a raera waka don girmanSa, Allah Mafi daukaka, a yi shelar madawwamiyar kaunarKa kowace safiya, amincinKa kuma kowane maraice, da abubuwan kade-kade masu tsarkiya da amon garaya mai dadi. Ya Ubangiji! Ayyukanka masu iko suna sa ni murna, saboda abin da Ka aikata ina rera waka domin farin ciki. AyyukanKa da girma suke, ya Ubangiji! TunaninKa da zurfi suke!

Ga wani abin da wawa ba zai iya sani ba, dakiki kuma ba zai iya ganewa ba, shi ne mai yiwuwa ne mugu ya yi girma kamar tsire-tsire, masu aikata mugayen ayyuka kuma su arzuta, duk da haka za a hallaka su ɗungum. Gama kai, ya Ubangiji!

Maɗaukaki ne har abada. Mun sani maƙiyanKa za su mutu, dukan mugaye kuwa za a yi nasara da su.

Ka sa ni na yi karfi kamar bijimi mai fada, Ka sa mini albarka da farin ciki. Na ga faduwar makiyana, Na ji kukan mugaye. Adalai za su yi yabanya kamar itatuwan giginya, za su yi girma kamar itatuwan al’ul na Lebanon. Za su zama kamar itatuwan da aka daddasa a Haikalin Ubangiji, suna ta yabanya a Haikalin Allahnmu. Wadanda suke yin ’ya’ya da tsufarsu, a kullum kuwa kore shar suke, suna da karfinsu kuma. Wannan ya nuna Ubangiji adali ne, Shi wanda Yake kare ni, ba kuskure a gare Shi.

(Zabura 90-92)