✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya yi wa Babban Limamin Kudancin Kaduna rasuwa

Sarkin ya rasu ya na da shekara 130 a duniya.

Babban Limamin Masarautar Jama’a da ke Karamar Hukumar Jema’a a Jihar Kaduna, Sheikh Adam Tahir, ya rasu yana da shekara 130.

Limamin ya rasu ne a yammacin ranar Laraba, bayan gajeruyar rashin lafiya, kamar yadda na’ibinsa Alhaji Muhammad Kabir D. Kassim, ya tabbatar.

Na’ibin nasa ya ce Sheikh Adam Tahir, wanda ya shafe shekaru yana jan Sallar Juma’a a Babban Masallacin Juma’a na Kafanchan, abin koyi ne ga jama’a.

Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II, ya bayyana rasuwar limamin a matsayin babban rashi ga Masarautar Jama’ar da kuma daukacin jama’ar Kudancin Kaduna.

Wasikar ta’aziyyar mai dauke da sa hannun sakataren masarautar, Alhaji Yakubu Isa (Dokajen Jama’a), ta bayyana kaduwa da samun labarin rasuwar limamin, wanda  kuma daya ne daga cikin masu nadin sarki a masarautar.

Masarautar ta kuma yi addu’ar samun rahama ga mamacin.

Ibrahim Adam Tahir, daya daga cikin ’ya’yan marigayin, ya shaida wa Aminiya cewar mahaifin nasu ya haifi ’ya’ya 50, amma 26 ne ke raye a yanzu, yana da jikoki 290 da tattaba-kunne sama da 200.

Za a yi masa Sallar Janaza da safiyar ranar Alhamis a Kafanchan.