✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Allah Ya yi wa hadimin Atiku rasuwa

Barista Abdullahi Nyako, hadimin dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya rasu.

Allah Ya yi wa Barista Abdullahi Nyako, hadimin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, rasuwa.

Atiku Abubakar, ya tabbatar da rasuwar Barista Abdullahi Nyako ne ta sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin a safiyar Alhamis.

“A madadin iyalina’, ina mika ta’aziyyarmu ga iyalan Abdullahi Nyako, tare da addu’a Allah Ya jikan shi Ya gafarta kurakuransa, Ya kuma sanya shi a Aljannah Firdaus.”

Atiku ya ce, “Mastayin Barista Abdullahi Nyako a wajena ta wuce ta hadimi; Dan uwana ne kuma ya hidimta min cikin amana da halarci.”